Daga AISHA ASAS
Kotun Majistare da ke zamanta a Magajin Gari, Jihar Kaduna, ta tattara, ta miƙa shari’ar da ake yi da fitaciyyar jaruma a masana’antar finafinai ta Kannywood, Hadiza Aliyu Gabon zuwa babbar kotun shari’a.
A ranar Juma’ar da ta wuce, Alƙali Isiyaku Abdulrahman, me jagorantar shari’ar da ake gwabzawa tsakanin jaruma Hadiza Aliyu Gabon da wani mutum zuwa Babbar kotun Musulunci da ke Tudun Wada.
Wannan ya biyo bayan zargin da alƙalin ke yi na lauyan mai ƙara na ƙoƙarin ɓata wa kotu lokaci, don haka ya ba shi zaɓi kafin yanke hukuncin.
“Kana da zaɓi biyu, ko dai in yi watsi da ƙarar, ko kuma in mayar da ƙarar zuwa wata kotu,” inji alƙali Isiyaku Abdulrahman.
Idan mai karatu bai matanta ba, a kwanakin baya mun tava kawo ma ku labarin rikicin da ya ɓarke tsakanin jarumar Kannywood Hadiza Gabon da kuma wani ma’aikacin gwamnati mai suna Bala Musa, wanda ya shigar da ƙara kan zargin wai ta masa zamba cikin aminci, ta ci kuɗinsa, amma ta ƙi auren sa kamar yadda ta yi masa alƙawari.
Bala Musa, ya maka jaruma Hadiza Gabon kotu saboda kuɗaɗen da ta tatsa wurin sa da zummar zata zama matar shi. Kuɗin wafanda ya ce, sun kai kimanin Naira 396,000 a cewar sa. Kuma ya shedawa kotu cewa, a duk sa’ilin da ta buqaci kuɗi, yana bata ba tare da ɓata lokaci ba, har adadin ya kai ga hakan.
Ita kuwa jarumar tuni ta ƙaryata zargin da Bala ke yi mata ta hannun lauyanta, ta tabbatar wa da kotu cewa, bata tava ma gani ko wata mu’amala da mai ƙarar tata ba.
Shi kuma Bala ya gabatarwa kotu shedar lissafin kuɗin da ya tura ta asusun banki tare da sanar da sunayen mutane huɗu da suka zama ‘yan aike tsakanin sa da jarumar.
Biyu daga ciki sun kasance makusantan jarumar ne, wato qawarta mai suna Fatima Abdullahi da kuma yaronta mai suna Abdullahi Yusuf. Dukkansu sun amsa laifin amfani da sunan jarumar suna yin sojan gona, har suna karɓar kuɗi da sunanta, sai dai sun nemi kotu da ta yi masu afuwa.
A ɓangaren lauyan jarumar, ya bayyana cewa, ya so ace kotu ta wanke jarumar kasancewar ita ɓata cuci kowa ba, kuma zargin zamba cikin aminci da aka yi mata bata aikata ba.
Wannan lamari dai ya yi dogon ƙarko, domin an yi zaman kotu har sau huɗu, sai dai ba a cimma matsaya ba, wannan ce ta sa, a wannan karon alƙalin ya bayyana mayar da shari’ar zuwa Babbar kotun Musuluncin.