Mutanen da suka fi taka rawar gani wajen samun ’yancin Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Jaridar Blueprint Manahaja ta yi bincike daga wurare daban-daban dangane da mutanen da suka fi taka rawa wajen fafutukar nema wa Nijeriya ’yanci. Za mu tattaro mutum bakwai waɗanda suka yi fice wajen samun ’yancin:

  1. Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto (Yuni 12, 1910 – Janairu 15, 1966):

An haifi Sir Ahmadu Bello a garin Rabbah na jihar Sokoto da ke arewacin Nijeriya. Sardauna na daya daga cikin jagororin Nijeriya da suka yi fice a duniya. Ahmadu Bello ya riqe sarautar Sardaunan Sokoto kuma ya jagoranci jam’iyyar Northern People’s Congress (NPC), inda ya mamaye harkar siyasar kasar a jamhuriya ta ɗaya.

Sir Ahmadu Bello ya yi fafutuka wajen nema wa Nijeriya ‘yanci, inda bayan dawowarsa daga wani bulaguro da ya yi zuwa Birtaniya, aka naɗa shi a matsayin dan majalisa mai wakiltar lardin Sokoto. A yau hoton Sardauna ne a kan kuɗin Nijeriya na Naira 200.

Wasu daga cikin abubuwan da ake tunawa da Sardauna sun haɗa da Jami’ar Ahmadu Bello University da ke Zaria wadda aka sanya mata sunansa da kuma rawar da ya taka wajen cigaban arewacin ƙasar.

  1. Cif Anthony Enahoro (22 Yuli 1923 – 15 Disamba 2010):

Cif Anthony Eromosele Enahoro na ɗaya daga cikin fitattun ‘yan gwawarmayar ƙin jinin mulkin mallaka kuma mai rajin kafa dimokraɗiyya. Mista Enahoro ya zama Editan jaridar Southern Nigerian Defender ta Nnamdi Azikiwe, inda ya zamo editan jarida mafi ƙarancin shekaru a Nijeriya.

Enahoro ne mutum na farko da ya fara miqa buƙatar neman ‘yancin kan Nijeriya a 953. Hakan ne ya sa ake yi masa laƙabi da “Uban Nijeriya”. Chief Enahoro masani ne kuma ya yi ta fafutuka kan Nijeriya har lokacin da ya mutu a 2010.

  1. Herbert Macaulay (14 Nuwamba 1864 – 7 Mayu 1946):

Sunansa Olayinka Herbert Samuel Heelas Badmus. Ya kasance ɗan kishin ƙasa, ɗan siyasa, Injiniya, mai ilimin tsara gine-gine kuma ɗan jarida ne kuma mawaƙi. ‘Yan Nijeriya da dama na bayyana shi da jagoran masu kishin ƙasar.

Mista Macaulay ya yi suna wajen hamayya da mulkin turawan mulkin mallaka. A shekarar 1919, ya tsaya wa masu sarauta a London waɗanda aka kwace wa gonaki inda ya tilasta wa gwamnatin turawan mallaka da ta biya sarakan diyya.

Hakan ne ya fusata Majalisar Birtaniya ta British Council inda har ta kai ga ta ɗaure shi sau biyu. Macaulay ya shahara inda a ranar 24 ga watan Yuni 1923 ya kafa jam’iyyar siyasa ta farko a Nijerita ta Nigerian National Democratic Party (NNDP). Herbert Macaulay ya mutu a 1946 to amma hotonsa ne a tsohuwar Naira 1.

  1. Cif Obafemi Awolowo (6 Maris 1909 – 9 Mayu 1987):

Cif Obafemi Jeremiah Oyeniyi Awolowo ɗan kishin kasa ne kuma dattijo wanda ya taka muhimmiyar rawa a gwagwarmayar neman ‘yancin kan Nijeriya. Shi ne firimiyan yankin kudu maso yammacin Nijeriya na farko sannan ya yi kwamishinan kuɗi a gwamnatin tarayya. Cif Obafemi ya zama mataimakin shugaban qasa na majalisar zartarwa a lokacin yaƙin basasa. Awolowo ya jagoranci masu hamayya na jam’iyyar Action Group a majalisar dokokin tarayya. Duk da cewa bai ci takarar shugabancin Nijeriya a jamhuriya ta biyu ba, Cif Awolowo ya kasance ɗan takara na biyu mai yawan ƙuri’a bayan Alhaji Shehu Shagari. Hoton Obafemi ne a jikin Naira 100.

  1. Funmilayo Ransom Kuti (25 Oktoba 1900 – 13 Afrilu 1978):

Funmilayo Ransom Kuti ta kasance mace ɗaya tilo a jerin sunayen ‘yan gwagwarmayar neman ‘yancin kan Nijeriya. Fumilayo ta kasance malamar makaranta, ‘yar siyasa, mai fafutukar kare ‘yancin mata sannan kuma mai riƙe da sarautar gargajiya. Ita ce mahaifiya ga shahararren mawaƙin nan na Nijeriya, Femi Kuti. Funmilayo ce mace ta farko da ta fara tuqa mota a Nijeriya. An zaɓe ta a majalisar sarakunan gargajiya, inda ta kasance wata wakiliya ta al’ummar Yarabawa. Fafutukar da ta yi ta janyo wa ‘ya’yanta bakin jini musamman lokacin gwamnatocin soji.

  1. Nnamdi Azikwe (16 Nuwamba 1904 – 11 Mayu 1996):

Chif Benjamin Nnamdi Azikiwe ne jagoran ‘yan gwagwarmayar masu kishin ƙasa na zamani. Nnamdi wanda ake yi wa laƙabi da mai kishin ƙasa ya riƙe Editan jaridar African Morning Post. Shi ne mutum farko ɗan Nijeriya da sunansa ya shiga Majalisar Tuntuva ta Amurka. Bayan ayyana Nijeriya a matsayin Jamhuriya, Dr Nnamdi Azikwe ya yi bakin ƙoƙarinsa wajen ganin ya haɗa kan ƙasar. Dr Zik ya zamo shugaban Nijeriya na farko.

  1. Tafawa Ɓalewa (Disamba 1912 – 15 Janairu 1966):

Alhaji Sir Abubakar Tafawa Balewa ne Firayin ministan Nijeriya na farko nayam da ƙasar ta samu ‘yancin kai a 1960. An zabi Sir Abubakar Balewa a matsayin ɗan majalisar dokokin lardin Arewa a 1946, sannan ya je majalisar dokoki ta tarayya a 1947. Tafawa Balewa ya zamo ɗan majalisa mai rajin kare Arewacin Nijeriya. Alhaji Abubakar Tafawa Balewa tare da Sardaunan Sakkwato sun kafa jam’iyyar Northern People’s Congress (NPC).