An sake tura sabon Kwamishinan ‘Yan Sanda a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano

Babban Sufeton ‘Yan Sandan Nijeriya, Usman Alkali Baba, ya turs CP Ahmad Kontagora, zuwa Kano a matsayin sabon Kwamishinan ‘Yan Sanda da zai jagoranci gudanar da zaɓen gwamna da na ‘yan majalisar dokoki na jihar.

Wannan ya biyo bayan dakatar da turo CP Feleye Olaleye da Babban Sufeton ‘Yan Sandan ya yi, bayan an turo shi a makon da ya gabata a matsayin Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano.

A ‘yan kwanakin nan dai rundunar ‘yan sandan ta turo kwamishinonin ‘yan sanda akai-akai zuwa Jihar Kano, wanda ya janyo ƙorafi da gudanar da zanga-zanga daga magoya bayan jam’iyyar adawa ta NNPP, sakamakon yunƙurin turo tsohon babban jami’in tsaron gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje wato CP Balarabe Sule, wanda shi ma aka dakatar da turo shi.

Duba da ƙaratowar zaɓe ana ganin wannan shi ne zai iya zama na ƙarshe har ya zuwa bayan zaɓen da zai gudana ranar Asabar mai zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *