An naɗa alƙalin da zai saurari ƙarar ADC tsakanin David Mark da Nafi’u Bala

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Babban alƙalin kotun tarayya ya sake tura ƙarar da ke ƙalubalantar shugabancin jam’iyyar ADC zuwa hannun wani sabon alƙali domin ci gaba da sauraron shari’ar. Ƙarar dai Nafiu Bala, tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa, ne ya shigar yana ƙalubalantar halaccin shugabancin riƙon ƙwarya ƙarƙashin jagorancin Sanata David Mark.

An mayar da shari’ar ga Mai Shari’a Peter Lifu bayan tsohon alƙalin da ke saurarar ƙarar, Emeka Nwite, ya kasance cikin alƙalan da majalisar kula da harkokin shari’a ta ƙasa (NJC) ta ba da shawarar a naɗa su a matsayin alƙalan kotun ɗaukaka ƙara. Nafiu Bala na neman kotu ta hana David Mark, Rauf Aregbesola da sauran mambobin kwamitin gudanarwa na riƙon ƙwarya ci gaba da jagorantar jam’iyyar.

A cikin ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/1819/2025, Bala ya yi zargin cewa kafa shugabancin riƙon ƙwarya ya saɓa wa kundin tsarin mulkin ADC da kuma dokar zaɓe. Waɗanda ake ƙara sun haɗa da jam’iyyar ADC, David Mark, Rauf Aregbesola, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) da kuma tsohon shugaban jam’iyyar, Ralph Nwosu.

A zaman da aka yi a baya, lauyan Bala ya buƙaci a canja alƙalin da ke sauraron ƙarar, matakin da lauyoyin ɓangaren masu kare kai suka soki suna mai cewa hakan na iya jinkirta shari’ar. Daga bisani, Mai Shari’a Nwite ya ɗage sauraron ƙarar ba tare da sanya sabuwar rana ba, yana jiran kwafin hukuncin kotun ƙoli kafin ci gaba da shari’ar.

By ukarofi

Leave a Reply