An rantsar da Donald Trump a matsayin shugaban Amurka na 47

Tsohon shugaban ƙasa na Amurka, Donald Trump, ya sake ɗarewa kan kujerar shugabancin ƙasar a matsayin shugaban ƙasa karo na biyu, a wani abin tarihi da ya faru ranar Litinin. Trump, wanda ya rantsar da kansa a gaban Majalisar Dokoki ta Amurka, ya sha alwashin ɗaukar matakai masu tsauri kan batutuwan shige da fice da kuma al’adun ƙasar, yana mai cewa zai fara gaggawar soke dokokin tsohon shugaban ƙasa Joe Biden.

Taron rantsarwar, wanda aka gudanar a cikin ɗaki saboda tsananin sanyi, ya samu halartar manyan mutane da suka haɗa da shugabannin kamfanoni kamar Elon Musk, Mark Zuckerberg, Jeff Bezos, da Sundar Pichai. Wannan karon, Trump ya samu kyakkyawar tarba daga Joe Biden, wanda ya ce, “Barka da dawowa gida,” lokacin da suka gana a fadar White House kafin su tafi majalisar dokoki.

A jawabin sa, Trump ya bayyana cewa zai ayyana dokar ta-ɓaci a kan iyakar Amurka da Mexico domin daƙile haramtattun ‘yan gudun hijira, tare da bayar da damar sojoji su taka rawa wajen kare iyakar.

Haka kuma, ya yi alƙawarin cire dokar da ta ba wa duk wanda aka haifa a Amurka damar zama ɗan ƙasar kai tsaye, tare da kawo sauye-sauye kan dokokin bambancin jinsi da kuma shirin daidaito a hukumomin gwamnatin tarayya.

Trump ya bayyana wannan wa’adin nasa a matsayin sabon babi ga Amurka, yana mai cewa zai ɗauki matakai cikin sauri da ƙarfin gwiwa don magance dukkan matsalolin da suka addabi ƙasar. A yayin taron bikin ƙaddamarwa, ya ce zai kawo ƙarshen “shekaru huɗu na koma bayan Amurka,” tare da nuna ƙudurin kawo sauyi cikin hanzari.