An rantsar da shugabannin tsangayoyin karatu na Kwalejin Sa’adatu Rimi

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano

A ranar Litinin ne aka rantsar da shugabannin tsangayoyin karatu da shugabannin darusa ko kwasakwasai da ke kwalejin Sa’adatu Rimi a Kano.

Dakta Kabiru Ahmad Gwarzo, shugabanta a wani taro da aka yi wanda ya haɗa da Hadi Bala babban sakatare a ma’aikatar ilimi mai zurfi wanda ya wakilci kwamishinan ma’aikatar Hon. Yusuf  Kofar Mata, sai sheikh Aminu Daurawa a matsayin babban malami mai nasiha akan shugabanci, da dai sauran manyan shugabannin sassa na makarantar da su ka kammala wa’adin shugabancin su a tsangayoyin na kwalejin sa’adatu Rimi.

Shugaban nin dai da aka rantsar na tsangayoyin da ke Sa’adatu Rimi su ne, Darka Ali Abdu Gezawa tsangayar ilimin manya a matsayin shugaba sai Dakta Mahe Isah Adam tsangayar ilimin harsuna, Malam Aminu tsagayar ilimin sana’o’i, Malam Muhammad Zubairu Tsangayar ilimin Sakandire, sauran su ne, Malam Lawan Yakubu tsangayar nazarin kimiyya, sai Malam Auwalu Inusa ilimin matakin farko a yayin da Malam Nura Yau ke cikin mataimakan ɗaya daga cikin tsangayoyin da aka rantsar da shugaban tsangayoyin da kuma shugaban nin darusa da kwalejin ke da su.

A jawabinsa Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyana matsayin shugabanci a shari’ar musulinci a matsayin babban al’amari ne da ke buƙatar gaskiya, Amana, Tausayi, da kuma sa’ido na ganin komai ya tafi dai dai ta hanyar karrama wanda ya yi bajinta da ƙoƙari a shugabancinsa da sauran dabaru na tafiyar da mulki.

A ƙarshe shugaban kwalejin Sa’adatu Rimi Dakta Kabiru Ahmad Gwarzo ya bayyana farin cikinsa da wannan rana da kuma irin cigaban da wannan makaranta ta samu a wannan lokaci na mulkin Alhaji Kabiru Yusuf, da kwamishinan ma’aikatar ilimi mai zurfi da sauran masu ruwa da tsaki da kuma irin canje canjen da aka samu shi ne babbar masalahar cigaban kwalejin ga kuma cigaban da aka samu na cewa kwalejin ta samu sahalewar hukumomi masu ruwa da tsaki wajan yin karatunn Digiri a ƙashin kanta wanda a baya ta na da haɗin gwiwa ne da jami’ar Bayero BUK, da ABU da jami’ar, NWU, mallakar kano wanda yanzu akwai ɗalibai sama da 2000 da su ka kusa kammala karatu a wannan tsari na haɗin gwiwa da jami’o’i