An sace jami’an INEC kan hanyarsu ta zuwa cibiyar tattara sakamakon a Zamafara

Daga WAKILINMU

Bayanai daga Jihar Zamfara sun ce an yi garkuwa da jami’an zaɓe a kan hanyarsu ta zuwa cibiyar tattara sakamako a yankin Ƙaramar Hukumar Maradun.

Ƙaramar Hukumar Maradun nan ne mahaifar Gwmanan Jihar, Bello Mohammed Matawalle mai neman ta-zarce a shugabancin jihar.

Jami’an na hanyarsu ta zuwa hedikwatar INEC da ke Gusau, babban birnin jihar, don miƙa sakamakon zaɓen gwamna na yankin Maradun.

An ce bayan kama su da aka yi, an tafi da jami’an zuwa wani waje wanda ba a bayyana ba.

Kakakin INEC a jihar, Muktari Janyau, ya shaida wa jaridar Daily Trust cewar an sanar da ‘yan sanda abin da ya faru.

“Kwamishinan Zaɓe na jihar, Farfesa Sa’idu Babura Ahmed, ya kai wa ‘yan sandan rahoton abin da ya faru don ɗaukar matakin da ya dace,” in ji Janyau.

Sai dai an sako su a daren jiya har sun kai sakamakon zaɓen, wanda hakan shine ya bayar da damar da aka sanar da sakamakon da ya bai wa PDP da ɗan takararta a jihar, Dauda Lawal Dare, nasarar lashe zaɓen.