An sake tono asirin Amurka

Daga CMG HAUSA

Jami’ar Stanford ta ƙasar Amurka da wani kamfanin nazarin yanar gizo sun ƙaddamar da rahoton bincike a watan jiya cewa, cikin shekaru kusan 5 da suka gabata, Amurka ta baza labaran bogi ta hanyar amfani da shafukan kafafen sada zumunta da dama, waɗanda suka yayata kalaman amincewa da ƙasashen yammacin duniya, da ɓata sunan ƙasashen Sin da Rasha da Iran da dai sauransu.

rahoton ya yi nuni da cewa, mai yiwuwa ne rundunar Amurka ce take aika wannan ɗanyen aiki.

Yanzu kuma an rufe waɗannan shafuka duka.

Har kullum Amurka ta ƙware wajen ƙirƙiro labaran bogi, da kawar da hankulan al’umma daga gaskiya.

Aikin da jami’ar Stanford da sauran hukumomi suka yin a bankaɗo wannan barna a fili, wani ɓangare ne na yaki da baza labaran bogi a yanar gizo da Amurka take yi, wadda ke ƙulla maƙarƙashiya a fannoni daban daban, alal misali, hambarar da gwamnatin ƙasashe, da rura wuta don samun riba ta hanyar ƙirƙiro da baza labaran bogi, da dora wa wasu laifi, da shafa wa abokan gaba da ke adawa da tunaninta baƙin fenti.

Lalle Amurka da ta daɗe tana ƙirƙiro ƙarya da mayar da baƙi fari, kuma ba a gaskata ta ba.

Mai fassara: Tasallah Yuan