Darasi a hirar Marigayiya Ummita da Sheikh Daurawa

Daga RAHMA ABDULMAJID

An ga wani faifan bidiyo ya fantsama inda a ciki Malam Aminu Daurawa yake bayyana tattaunawar su da Marigayiya Ummita (Ummu Kulthum) kwanaki kaɗan kafin mutuwarta.

Kalmomi uku ne suka maƙale a zuciyata cikin bayanin malamin a bidiyo mai tsawon kusan minti bakwai wato cewar ta:

“Ina so zan auri wani ɗan Chana amma iyayena sun ƙi yarda”

“Malam mutumin ya musulunta”

“Malam ina ta neman ka”

Waɗannan maganganu biyu sun ja hankalina ga wasu tambayoyi kamar haka:

1 Mai yaudarar ɗan Chana tana cin kuɗinsa ba da niyyar aure ba (kamar yadda ake bayyanawa a soshiyal midiya) ita ce take neman fatawar aure, har ta kira wani Malami, har ta ce sun yi magana da iyayen mai neman auren a Chana?

2 “Iyayena sun ƙi yarda”. To su waye iyayen? Ina jin ba ita ce yarinyar da aka ce ba ta da tarbiya ba? ‘Yar mace ce? To ta ina ta sami tarbiyar jin maganar iyayenta a kan aure har da za su iya hanawa? Su wanene iyayen? Macen? Su da basu iya tarbiya ba ma ta ina za su sami tunanin hana ‘yarsu auren wanda ba a san kowa nasa ba?

3 “Ya musulunta”. Ta dalilin wa aka sami musuluntar ɗan Chana? Ta dalilin yarinya mara tarbiya? Ta ina ma ta samu tarbiyar ba za ta auri na miji ba sai ta musuluntar da shi?

4 “Malam ina ta neman wayarka ban samu ba”. Ina mara tarbiya da shiriya za ta riqa neman malami babba haka ba ta gaza ba har sai da ta samu duk saboda ta bi tsarin addini wajen auren wani da kuma bin dokar iyayenta?

Zuwa yanzu waɗanda suka zazzagi Marigayiyar da aka yi wa kisan gilla, sannan suka aibata iyayenta da ke cikin tsananin ciwon rashinta, sannan suka riqa nuna kowa bai da tarbiya sai su, yaya za su ji da wannan nauyin?

Mu je ma a wannan yarinya ba ta da tarbiyya yaudara ta yi, shin hukuncin laifin yaudara shi ne kisa? Ina koyarwar Annabi SALLALLAHU ALAIHI wasallam da ke cewa masu tarbiya “ku riƙa tunawa da rera ambaton da kyawawan ayyukan mamatanku?” Su da basu bi wannan umarnin ba su ne masu tarbiya?

Duk zunubin wannan Marigayiya ta sami shahada don kashe ta aka yi wani ya kwashe mata zunubin. Kai da kake raye baka san ƙarshenka ba ma, wataƙil kai za ka kashe, wataƙil kana tsaka da savo ka mutu ( Allah Ya kiyaye), kai ne mai aibata mamaci? Kuma kai ne me tarbiya.

Shin ina ma tarbiya ga wanda baya iya tausayawa rai har a lokacin da ta bar gangar jiki irin nasa? Yarinya marainiya da uwarta, uwar marayu da ta zauna ta raine ta, baka bibiyi halin da uwar ta shiga wajen wahalar rainon marayu ba, baka taimaka ba, iyakar abinda ka sani shi ne, ka ƙara mata da zagi da zargi a lokacin da ta sake rasa wani rai ɗin bayan na uban ‘ya’yanta kai ne mai tarbiya ko?

Wato da dama cikin mu bambancinmu da Marigayi Shekau rashin bindiga. Allah Ya kyauta…. Allah Ya rage mana wannan baƙar zuciya.

Rahma Abdulmajid marubuciya ce, kuma mai sharhi a kan al’amurran
yau da kullum. Ta rubuto daga Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *