An sake tsinke Shugaban Faransa, Macron, da mari

Daga WAKILINMU

Rahotanni sun ce an tsinka wa Shugaban Ƙasar Faransa, Emmanuel Macron, mari a baina jama’a.

An ce abin al’ajabin ya faru ne a ranar Lahadin da ta gabata.

Wani hoton bidiyon da aka yaɗa soshiyal midiya ya nuna yadda wata mata ta sharara wa Macron mari inda jami’an tsaro suka hanzarta ɗaukar mataki.

Sai dai babu cikakken bayani dangane da matar da kuma dalilin da ya sa ta aikata hakan.

Wannan shi ne karo na biyu da Shugaban ke fuskantar irin wannan a baina jama’a.

Ko a Yunin 2021, wani mutum mai suna Damien Tarel, ya tsinka wa Macron ɗin mari a yankin Kudancin Faransa yayin da yake wani rangadi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *