An sako Dariye da Nyame daga kurkuku

Daga BASHIR ISAH

An sako tsoffin gwamnonin Jihar Filato da Taraba, wato Sanata Joshua Dariye da Jolly Nyame daga Gidan Gyaran Hali na Kuje, Abuja.

Majiyar Jaridar Daily Trust ta ce, an sako tsoffin gwamnonin ne da misalin ƙarfe 2:15 na rana a ranar Litinin.

Idan ba a manta ba, a zaman da dattawan ƙasa suka yi watanni huɗu da suka gabata ƙarƙashin agorancin Shugaba Muhammadu Buhari, Majalisar ta amince da yi wa su biyun afuwa.

Majiyar ta ce, “An yi musu afuwa ne bisa dalilin rashin lafiya da tsufa da ɗa’ar da suka nuna a zaman kurkukun da suka yi.”

Da aka nemi jin ta bakinsa kan sakin, Mai Magana da Yawun Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali na Abuja, Chukwuedo Humphrey, ya tabbatar da hakan.

An yanke wa Nyame zaman kaso na shekara 12 bisa laifin karkatar da kuɗin gwamnati biliyan N1.64 a zamanin da yake Gwamnan Taraba, yayin da aka yanke wa takwaransa na Filato, Dariye, shekara 10 a kurkuku kan mundahanar biliyan N1.126.