CAN na adawa da sake gina kasuwar Jos da Bankin Jaiz zai aiwatar

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar Kiristocin Nijeriya (CAN) reshen Jihar Filato da haɗin gwiwar ƙungiyoyin ’yan asalin Jihar Filato da sauran ƙungiyoyi masu alaƙa da su, sun yi kira da a dakatar da aikin da ake shirin yi a babbar kasuwar Jos (Terminus) saboda abin da suka bayyana da rashin fahimta a yarjejeniyar kwangila.

A cewarsu, yarjejeniyar tana tsakanin gwamnatin jihar ne da mai kuɗin sake gina kasuwar – Bankin Jaiz Plc.

Ƙungiyar ta yi wannan kiran ne a wani taro da Shugaban Ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN) reshen jihar Filato, Rabaran Fr. Polycarp Lubo ya yi a ranar Litinin a gidan gwamnatin Jos.

Shugaban CAN ɗin ya bayyana matsayin masu ruwa da tsaki a wani taron manema labarai a ƙarshen taron da ƙungiyoyin da shugabannin gwamnatin Filato suka yi.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya tuna cewa, majalisar zartarwar jihar Filato ta amince da sake gina kasuwar da gobara ta tashi a shekarar 2002 ta hanyar haɗin gwiwar jama’a na sirri da bankin Jaiz.

An yi kiyasin sake gina ginin zai ci Naira biliyan 9.4 a matakai uku na kasuwar.

Jami’in na CAN ya ce, ya kira taron ne biyo bayan tashin hankalin da jihar ka iya shiga kan samun labarin cewa jihar ta jinginar da rayuka da dukiyoyin matasanta na tsawon shekaru 40 bisa yarjejeniyar da ta ƙulla da bankin.

Ya ce, ƙungiyoyin sun ji takaicin rashin tuntuvarsu a matsayin masu ruwa da tsaki kafin yarjejeniyar sake gina kasuwar.

Ya kuma ba da shawarar a dakatar da aikin sake ginawa har sai an yi shawarwarin da ya dace.

“Mun cimma matsayar cewa su gwamnati za su je su gyara wannan lamarin, su duba damuwarmu har sai an shawo kan fargabarmu.

Da ya ke magana a madadin gwamnati, Chrysanthus Ahmadu, babban mai shigar da qara na jihar, ya nuna damuwarsa kan yadda aka yi wa mutanen Filato bayanin kwangilar sake ginawa.

Ya bayyana cewa, “shekaru 40 da suka wuce an ba da kwangilar masu saye don taimaka musu su kwato daga sayen shagunan.

“Yarjejeniyar ita ce hukumar da ke kula da kasuwar Jos za ta ba wa waɗanda aka raba kwangilar shekaru 40 a qarshen shekara 40 da kadarorin ta koma hannun hukumar kasuwar.

“Don haka idan kana sayen shago ka sani cewa kana sayen shekaru 40 ne, ba Bankin Jaiz ba ne wanda za a ba shekaru 40,” inji shi.

Ya ce, har yanzu gwamnatin jihar tana tattaunawa da bankin domin ba a cimma matsaya ba amma an samu fahimtar yadda za a gudanar da aikin.

Bankin Jaiz girma mai kuɗi ne kawai, yana sanya kuzi ne dan kwangila ya yi aikin kuma a ƙarshensa za su sayar da kashi 60 cikin 100 yayin da gwamnati za ta sayar da kashi 40 cikin 100,” inji shi.

Ya kuma bai wa al’ummar Filato tabbacin yin gaskiya da adalci wajen sayar da shagunan, inda ya ce ko kashi 60 cikin 100 da bankin zai sayar da shi gwamnati za ta sa ido a kai domin a yi adalci.

Ya ƙara da cewa, gwamnati ta saurari damuwarsu kuma za ta koma don ci gaba da tuntuvar juna domin cimma moriyar jama’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *