Yajin aikin ASUU: Gwamnati na neman raba kan malamai — NAAT

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar Malaman Fasaha ta Ƙasa (NAAT) ta ce, akwai lauje cikin naxi a rahoton Kwamitin Nimi Briggs kan abin da ya shafi yarjejeniyar ƙarin albashin ƙungiyoyin jami’o’in.

Ƙungiyar ta ce, ƙin sanya yarjejeniyar daidaita albashin da kwamitin ya yi a rahoton nasa, ba abin da zai haifar sai tsawaita yajin aikin ƙungiyoyin.

Shugaban ƙungiyar ta NAAT, Ineji Nwokoma ya zargi kwamitin da neman raba kan ƙungiyoyin ta hanyar bambamta tsarin albashinsu, saɓanin abin suka cimma a tattaunawarsu.

Ya ƙara da cewa, ko da sauran ƙungiyoyin jami’o’in sun janye nasu yajin aikin, to ɗakunan gwaje-gwaje da na lafiya, da gonakin makarantun za su kasance a rufe, matuƙar ba a gyara wannan matsala ba.

“NAAT za ta yi iya ƙoƙarinta wajen ƙin amincewa da bambamta albashin ƙungiyoyin duka, domin hakan zai haifar da wata matsalar ne bayan bai magance wata ba”.

“Don haka muna kira ga Kwamitin Nimi Briggs da ya dawo kan yarjeniyoyin da muka yi a zamanmu da su, saboda alamu na nuna ba shi da niyyar ɗaukar wani mataki a madadin Gwamnatin Tarayya”, inji shi.

Nwokoma ya kuma ce matakin gwamnatin na ƙin biyan albashin ma’aikatan saboda suna yajin aiki ya sava wa dokar Nijeriya.

A wani labarin kuma, Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta ce, Gwamnatin Tarayya ba za ta yi nasara ba a yunƙurinta na amfani da yunwa wajen tilastawa mambobinta komawa aji.

Shugaban ƙungiyar, Farfesa Emmanuel Osodeke ne ya bayyana haka a lokacin da ya bayyana a gidan talabijin na Channels na shirin Sunrise Daily.

Osadeke ya ce, tun bayan fara yajin aikin a watan Fabrairu, gwamnatin tarayya ta hana mambobinta albashi.

“An hana mu albashi. Wannan shi ne wata na shida da ake hana albashin mu,” inji shi.

“Sun yi tunanin cewa idan sun riƙe albashi na wata biyu ko uku, za mu zo bara mu ce ‘don Allah a bar mu mu koma bakin aiki’.

“Amma a matsayinmu na ƙungiyar masu hankali, mun girma fiye da haka. Ba za ku iya amfani da ƙarfin yunwa don ja da ‘ya’yanmu ba, abin da gwamnati ke yi ke nan.”

ASUU ta shiga yajin aikin gargaɗi ne bisa zargin ƙin biyan buƙatun ƙungiyar da suka haɗa da aiwatar da yarjejeniyar sulhun FGN/ASUU a shekarar 2009, tura UTAS, biyan basussukan da aka samu na Academic Allowances (EAA), ƙarin girma da kuma sakin albashin malamai da aka hana su.

A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne ƙungiyar ta ƙara tsawaita yajin aikin da wasu makonni huɗu, wanda hakan ya kawo cikas ga fatan ɗaliban na komawa makaranta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *