An samu cimma kashi 80 na yaƙi da garkuwa da mutane – Ribaɗu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

A ranar Alhamis ne mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Mallam Nuhu ya bayyana cewa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta samu sama nasara da kashi 80 cikin 100 a yaƙi da masu garkuwa da mutane.

Ya ce, an samu nasarar ne sakamakon sadaukarwar da jami’an tsaro suka yi da kuma aiki mai inganci da ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro ke yi.

Ribadu ya bayyana haka ne a wajen ƙaddamar da cibiyar yaƙi da ta’addanci ta ƙasa (NCTC) da ‘Multi-Agency Kidnap Fusion Cell’ (MAAKFC).

Hukumar ta NSA ta ce, har yanzu satar mutane na ɗaya daga cikin manyan matsalolin tsaro a ƙasar, wanda ya haifar da wahalhalu ga iyalai da dama, da kawo cikas ga harkokin tattalin arziki, da kuma kawo babbar barazana ga zaman lafiyar ƙasarmu.

Ya ce: “A cikin ƙanƙanin lokaci, a ƙasa da shekaru biyu, mun samu nasara kashi 80 cikin 100. Amma ba mu magana gaba ɗaya ba.

“Muna da sojoji da jami’an sauran jami’an tsaro da ke cikin daji, suna sadaukar da rayuwarsu don ganin ƙasar nan ta zama wurin zaman lafoya da kuma mayar da ita kan turba ta yadda za mu samu rayuwa ta yau da kullum cikin lumana.

“Su ne jaruman da ba a sani ba, mutane ba sa magana a kansu. Ya kamata a riƙa faɗin abubuwa da suke yi.

Ya kuma buƙaci jami’an tagawar fusion cell da aka zaɓo daga hukumomin tsaro daban-daban da ƙungiyoyin leƙen asiri da su yi amfani da ƙwarewarsu da kuma tashi tsaye wajen yaƙi da matsalar garkuwa da mutane a aasar.

Ribadu ya kuma buƙace su da su rungumi haɗin kai, su yi amfani da ilimin da suka samu don tabbatar da cewa kare rayuwar ’yan Nijeriya.

By ukarofi