Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Daya daga cikin manyan jam’iyyun adawa a Nijeriya wato Labour Party, ta faɗa halin ƙaƙa-ni-ka-yi duk da hukuncin Kotun ƙoli na baya-bayan nan, wanda aka shigar domin warware rikicin shugabanci da ke addabar jam’iyyar.
Rikicin dai ya kaure ne tsakanin shugabancin jam’iyyar ƙarƙashin jagorancin Julius Abure da kuma ɗaya ɓangaren wanda ya ayyana Nenadi Usman a matsayin shugabar riƙo.
Jam’iyyar Labour ta shiga rikicin ne, bayan rasuwar shugabanta na kasa, Alhaji Abdulkadir Abdulsalam a shekara ta 2020.
Inda ake ta saɓata juyata tsakanin masu goyon bayan shugabancin Julius Abure da masu ganin ya zama wajibi a sake lalen shugabancin bayan ƙarewa wa’adin shugabancin nasa.
Sai dai a hukuncin da Kotun ƙolin Nijeriya ta yanke, ta soke hukuncin kotun ɗaukaka ƙara, wadda ta amince da Julius Abure a matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa.
Kotun ta ce babu wata kotu da take da ‘yancin tsoma baki a rikicin shugabancin jam’iyya, kasancewar “lamari ne na cikin gida.”
ɗan takarar jam’iyyar a zaɓen shugaban Nijeriya na 2023, Peter Obi ya karkata ne ga ɓangaren da ya amince da Nenadi Usman a matsayin shugabar riƙo.
A watan Satumban 2024 ne ɓangaren nasu ya naɗa ta kan muƙamin bayan wani taro da ya gudanar.
Julius Abure ya yi fatali da taron da kuma naɗin da aka yi wa Nenadi.
Haka nan kuma bayan kimanin wata ɗaya da naɗin ne kotu ta amince da shugabancin Julius Abure.
Yanzu dai lamarin ya sake rincaɓewa tun bayan da kotun ƙoli ta yanke hukuncin cewa kotu ba za ta tsoma baki a rikicin jam’iyyar ba.
Dukkanin ɓangarorin biyu na iƙirarin cewa su ne kotu ta bai wa gaskiya.
ɓangaren Jam’iyyar LP ƙarƙashin jagorancin Julius Abure ta yi barazanar korar “duk wanda ke yi wa jam’iyyar zagon ƙasa a cikin gida”.
ɓangaren ya ambato mutane kamar gwamnan jihar Abia, Aleɗ Otti da kuma ɗan takarar shugaban ƙasar a zaɓen 2023 na jam’iyyar Peter Obi a cikin waɗanda matakin zai iya shafa.
Umar Farouk Ibrahim, wanda shi ne sakataren jam’iyyar ɓangaren Julius Abure, ya shaida wa BBC cewa suna sane da “yadda wasu daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar ke ƙoƙarin yi wa jam’iyyar zagon ƙasa domin suna ganin yadda suke kai komo a wasu jam’iyyun adawa.”
Ya ce, “Kowa ya riga ya sani cewa gwamnan jihar Abia Aleɗ Otti da kuma Peter Obi, ba sa tare da shugabancin jam’iyyar domin hakan ne ya sa suka garzaya kotu suka kai kara kan cewa ba su yarda da shugabancin jam’iyya ba,” inji Farouk Ibrahim.
To sai dai kuma a nasu ɓangaren waɗanda aka yi wa barazanar dakatar da su daga jam’iyyar ta Labour sun ce wannan abu da ɓangaren Julius Abure suke duk shure-shure ne.
Muhammad Ndimi Abdullahi, ɗaya ne daga cikin ‘yan’yan jam’iyyar Labour da ke ɓangaren su Peter Obi, ya shaida wa BBC cewa duk abin da ɓangaren su Abure da jama’arsa ke faɗa “shaci faɗi ne kawai.”
“Mu abin da muka sani cewa shugabancin jam’iyya na ƙarƙashin gwamnan Abia da mataimakinsa da ‘yan majalisunmu na tarayya da jam’iyyar Labour da mambobin ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC, wadannan a yanzu suke da hurumi da dama a jam’iyyarmu ta Labour.
“Shi Abure a yanzu wa’adin shugabancinsa a jam’iyya ya kare tuntuni dama an zaɓe shi ne a kan zai yi shekara guda, to ya gama, amma kuma ba ya son barin muƙamin, shi ya sa yanzu yake kawo rudani saboda ba ya son tafiya, ita kuma jam’iyya ba harka ce ta ra’ayi ba, harka ce ta cikin gida. Muna da masu fada a ji don haka su ne ke da wuka da nama na su zabi wadanda za su ja ragamar jam’iyya,” inji Muhammad Ndimi Abdullahi.
Wasu ‘yan jam’iyyar dai sun yaba wa da hukuncin na kotun ƙolin inda suka ce an yi adalci, wasu kuma na cewa hukuncin na buƙatar fassarar da ta dace daga masana.
