An sanya hannu kan yarjeniyoyin kasuwanci na biliyoyin kuɗaɗe yayin baje kolin na’urorin zamani na Chongqing

Daga CMG HAUSA

Rahotanni na cewa, an rattaba hannu kan manyan yarjejeniyoyin kasuwanci guda 7, waɗanda suka kai darajar kuɗin Sin yuan biliyan 212.1, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 31.1, yayin baje kolin na’urorin zamani mai laƙabin “Smart China Expo 2022”, wanda aka buɗe a ranar Litinin a birnin Chongqing, na kudu maso yammacin ƙasar Sin.

Yarjejeniyoyin kasuwancin dai sun ƙunshi fannonin samar da ababen hawa dake amfani da na’urori masu ƙwaƙwalwa, da fasahohin samar da manhajojin fasahar sadarwa, da fasahohin ƙirƙire-ƙirƙire, da amfani da na’urori wajen sarrafa kayayyakin masana’antu.

Ana kuma fatan yarjejeniyoyin za su ingiza ƙarfin birnin Chongqing, na cin gajiyar fasahohin kwaikwayon tunanin bil adama.

Mashirya baje kolin sun ce, dandalin ya mayar da hankali ga mayar da birnin Chongqing wuri da zai bunƙasa fasahohin tattara manyan bayanai, da zurfafa haɗin gwiwa tare da manyan kamfanonin cikin gida da na waje.

Cikin manyan yarjejeniyoyin kasuwanci da aka sanyawa hannu, akwai guda 54 na kuɗin Sin yuan biliyan 1 ko wannen su.

Taken baje ƙolin shi ne “Fasahohin zamani: ƙarfafa tattalin arziki, kyautata rayuwa”.

Za a shafe yini 3 ana baje kolin, mai ƙunshe da ayyuka daban daban, ciki har da tarukan tattaunawa 20, yayin da za a gabatar da bayanai 120 game da wasu sabbin hajoji da fasahohi.

Kazalika za a gudanar da gasanni 10 masu nasaba da baje kolin.

Fassarawar Saminu Alhassan