Marigayi Alhaji Dakta Shehu Idris

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji (Dr.) Shehu Idris na ɗaya daga cikin manyan sarakunan Arewancin Nijeriya. Mai martaba sarki mutum ne masani, sannan kuma abin girmamawa a duk faɗin Arewa. Yana da karimci.

Ɗaya daga ciki ɗimbin hikimomi da Allah ya yiwa mai martaba sarkin Zazzau, Alhaji (Dr.) Shehu Idris ita ce tafiya da mutanen a cikin mulkinsa, yakan tuntuvi jama’a a kan abubuwan da ka je.

An haifi mai martaba sarkin Zazzau, Alhaji (Dr.) Shehu Idris a shekarar 1937. Shi ɗa ne ga Malam Idris Autan Sambo, shi kuma ɗan sarkin Zazzau na 10, Malam Muhammadu Sambo, shi kuma ɗan sarkin Zazzau na 3 Malam Abdulkarimu Bakatsine.

Karatunsa:

Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji (Dr.) Shehu Idris, ya fara karatunsa na addini tun yana ɗan shekara biyar a hannun malam Bawa da kuma malam Abubakar da ke Unguwar Iya a garin Zariya.

A shekarar 1947, lokacin yana da shekaru 11, Mai Martaba sarki ya fara karatun zamani a makarantar elimantare ta Zariya (Zaria Elementary School), daga nan kuma sai makarantar midil ta Zariya (Zaria Middle School) daga shekarar 1950 zuwa 1955. Bayan kammala wannan karatu nasa sai kuma ya wuce zuwa makarantar horas da malamai ta Katsina (Katsina Training College) inda ya gama a shekarar 1958.

Gogayyar aiki:

Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji (Dr.) Shehu Idris, ya fara karantarwa bayan kammala karatunsa na Katsina. Ya fara da koyarwa a makarantar firamare ta garin Hunƙuyi a shekarar 1958, daga nan kuma sai aka mayar da shi garin Zangon Aya, sannan sai Paki duk a matsayin shugaban makaranta (Head Master). Sannan kuma aka dawo da shi Zariya a matsayin shugaban makarantar firamare ta Ƙaura.

A shekarar 1960 ya zama magatakardar Sarkin Zazzau Marigayi Alhaji Muhammadu Aminu (Personal Secretary to the Emir of Zazzau). Daga baya kuma ya zama magatakardar Hukumar gargajiya >(Secretary to the Zaria Native Authority council) a shekarar 1963. Sannan kuma an yi masa naɗin Ɗanmadamin Zazzau, Hakimin Birni da Kewaye a shekarar 1963, muƙamin da ya riqe har zuwa zamowarsa sarki.

Zamowarsa sarki:

A shekarar 1975, bayan rasuwar Mai Martaba Sarkin Zazzau Alhaji Muhammadu Aminu, sai masu zaven sarkin Zazzau suka zavi Mai Martaba Sarki Alhaji (Dr.) Shehu Idris a matsayin sabon sarkin Zazzau, zaɓen da ya samu amincewa daga gwamnatin Jihar Tsakiyar Arewa wacce ke da helikwata a Kaduna, a zamanin mulkin Gwamna Manjo Abba Kyari. Wannan naɗi nasa shi ya mai da shi sarkin Zazzau na 18 a jerin sarakunan Fulani, sannan kuma sarki na 3 a zuriyar Katsinawa.

Rasuwarsa:

Marigayi Shehu Idris ya rasu yana da shekara 84, bayan shafe shekara 45 kan karagar mulki a Masarautar Zazzau.

Ya rasu ne da misalin ƙarfe 11:00 na safe agogon GMT+1 a ranar 20 ga Satumba, 2020, a asibitin Sojojin Nijeriya na 44 da ke Jihar Kaduna.