Daga JAMEEL GULMA a Kebbi
Gwamnatin Jihar Kebbi ta bayar da sanarwar sauke dukkanin sakatarorin hukumomin ilmi 21 a faɗin jihar.
Sanarwar tana ƙunshe ne a wata takarda mai ɗauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar Alhaji Yakubu Bala Tafida ranar Litinin ɗin nan.
Takardar ta nuna cewa an umarci duk sakatarorin hukumomin ilmin da su miƙa ragamar jagorancin hukumomin ga shugabannin sassan gudanarwa da ke ma’aikatar ba tare da ɓata lokaci ba.
Haka-zalika sakataren gwamnatin jihar ya bayyana godiyar gwamnatin jihar ga tsofaffin sakatarorin hukumomin ilmin bisa irin gudummawar da suka bayar wajen cigaban ilmi.
Haka-zalika ya bayyana cewa kowane tsohon sakataren Ilmi da ya koma ma’aikatar sa ta ainihi da aka ɗauko shi.