Daga USMAN KAROFI
Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed, ya bayyana alhininsa bisa rasuwar fitacciyar ‘yar jarida, Hafsat Adebayo, wacce ta rasu bayan jinyar dogon lokaci. A wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Mukhtar M. Gidado, ya fitar, gwamnan ya ce rasuwarta babban rashi ne ga ‘yan jarida ba kawai a Bauchi ba, har ma ga Najeriya baki ɗaya. Ya bayyana marigayiyar a matsayin jajirtacciyar ‘yar jarida wadda ta ba da gudunmawa matuƙa wajen inganta aikin jarida na gaskiya da riƙon amana.
Gwamna Bala ya jinjinawa marigayiyar bisa irin rawar da ta taka a fagen yaɗa labarai, inda ya ce ta kasance ƙwararriyar ‘yar jarida da ta yi aiki tuƙuru wajen watsa sahihan labarai da ƙarfafa ingantaccen tattaunawa a cikin al’umma. Ya ce jajircewarta da sadaukar da kai a wannan fanni zai ci gaba da zama abin koyi ga sauran ‘yan jarida, musamman masu tasowa.
Hakazalika, gwamnan ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayiyar da ƙungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) reshen Jihar Bauchi, yana mai addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki ya gafarta mata, ya ba ta Aljannar Firdausi, tare da bai wa iyalanta haƙurin jure wannan babban rashi.
