Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta buƙaci tsohon Kwamishinan zaɓe na Jihar Adamawa, Hudu Yunusa Ari, da ya kare kansa a gaban kotu maimakon shirya taron manema labarai. Ari, wanda ya koma ƙasar bayan zargin aikata ba daidai ba a zaɓen gwamnan Adamawa na 2023, ya dawo kuma ya bayyana a taron manema labarai cewa Sanata Aisha ‘Binani’ Ɗahiru ta jam’iyyar APC ce ta lashe zaɓen.
Mai magana da yawun shugaban INEC, Rotimi Oyekanmi, ya mayar da martani kan ikirarin Ari, yana mai cewa babu wani sabon abu a cikin bayanan da ya fitar. Ya jaddada cewa batun sakamakon zaɓen ya rigaya ya kammala a kotuna, daga Kotun sauraron ƙararrakin zaɓe zuwa kotun ɗaukaka ƙara har zuwa Kotun ƙoli.
INEC ta ce ba za ta yi sharhi kan halayyar Ari a lokacin kammala zaɓen ba, kasancewar lamarin yana gaban kotu a Yola. Hukumar ta buƙaci Ari da ya bi hanyar doka domin kare kansa, tun da ya dawo gida, maimakon yin maganganu a kafafen watsa labarai. A baya-bayan nan, Majalisar dattawa ta amince da buƙatar Shugaba Bola Tinubu na sauke Ari da wasu kwamishinonin zaɓe daga Abia da Sokoto bisa zargin aikata ba daidai ba.
