
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Tarayya tana sanar da al’umma cewa ta buɗe ƙofar neman sabon akanta-janar da manyan sakatarori don cike gurabe a Jihar Oyo da shiyyar Arewa-maso-Yamma.
Shugabar Ma’aikatar ma’aikata, Misis Didi Walson-Jack ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a Abuja, ranar Litinin.
Ta ce za a bada ayyukan ne ga waɗanda suka cancanta bayan bi ta hanyoyin tantancewa, waɗanda suka haɗa da rubuta jarrabawa, wadda za a yi ƙarƙashin wata babbar hukumar tsaro ta Gwamnatin Tarayya.
Haka kuma manyan sakatarorin da suka yi ritaya ne za su jagoranci nazari da fitar da sakamakon jarrabawar.
Za kuma a gudanar hakan ne kasancewar Akanta-Janar, Dakta Oluwatoyin Sakirat Madein za ta yi ritaya a watan Maris na shekarar 2025.
Jami’an gwamnati da ke matsayi na 17 kuma suka shekara biyu da matsayin ne kaɗai suka cancanci neman muƙamin.
Sannan a ɓangaren masu neman guraben sakatarori, sai mutum ya cika ƙa’idodin da aka gindaya na tantancewa kafin a tabbatar da shi.
Matakan tantancewar sun haɗa da na kwamitin manyan sakatarori, wanda jami’an ICPC da na DSS za su lura da shi.
Sai bayyana kadarori, wanda za a gabatar ƙarƙashin Cibiyar kula da Ladabin Ma’aikata ta CCB.
Sauran sun haɗa da bincike game da hannu a rashawa, rubuta jarrabawa, ƙwarewa ta fuskar amfani da kwamfuta da sauran su.
