An tsinci jariri a cikin kango a garin Birnin Kebbi 

Daga JAMEEL GULMA a Kebbi

Ranar Larabar da ta gabata mutanen Unguwar Nahuta da ke cikin garin Birnin Kebbi fadar jihar sun wayi gari da wani abin al’ajabi inda suka ga wani jariri sabon haihuwa a wani kangon gida.

Wani mazauni unguwar da bai so a bayyana sunansa ya bayyana cewa kukan jinjirin ne ya janyo hankalin mutanen da ke zaune kusa da wajen inda ko da suka je suka same shi cikin tufafi sababbi an saka shi a cikin zani kuma da alamar fenti a fuskarsa.

Ya ƙara da cewa daga nan ne dai suka yanke shawarar kai rahoto a ofishin Hisbah.

Hukumar Hisbah ta Jihar Kebbi ta shafinta na Facebook ta tabbatar da faruwar lamarin inda kuma ta yi kira ga al’umma da su rinƙa saka ido ga lamurran da ke faruwa a cikin unguwanninsu tare da kai rahoton duk wani abu ko waɗansu mutane da ba su yarda da su ba ga hukuma.

Haka kuma hukumar ta bayyana cewa za ta kula da wannan jinjirin kamar yadda ta saba har sai yadda hali ya yi kuma tana neman al’umma da su taimaka wajen ganin an gano matar da ta yar da wannan jinjirin.

Haka-zalika hukumar ta Hisbah ta bayyana cewa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ganin an zaƙulo irin waɗannan ɓatagarin da ire-irensu tare da ɗaukar matakin da duk ya kamata, saboda haka ta nemi haɗin kan al’umma da su ma akwai rawar da ya kamata a ce suna takawa don ganin hukumar ta  samu nasarar aiwatar da ayyukanta a faɗin jihar ta Kebbi.

Wani magidanci da ke zama a wata unguwa da ke wajen garin Birnin Kebbi ya bayyana wa wakilinmu da cewa yar da jijirai ba wani sabon abu ba ne saboda yana da wahala a ɗauki wata ɗaya ba a samu jinjirin da aka yar ba ko dai a raye ko kuma ya mutu ko kuma an jefa a rijiya ko an binne shi.