Daga GAMBO ISAH
Shugaban ƙungiyar NURTW reshen ƙaramar Hukumar Bama a Jihar Borno, Alhaji Ba Mai Mustapha, a cikin wata sanarwar manema labarai da ya raba wa jaridun Blueprint a Abuja, ya yaba da ɗimbin nasarorin da Maigirma Gwamnan Jihar Borno ya samu da kuma salon shugabanci a fannin gina hanyoyi, tsarin kiwon lafiya, samar da kayan aiki ga jami’an tsaron soji, ‘yan sanda da JTF a dukkan ƙananan hukumomi 27 da ke faɗin jihar, da dai sauransu.
Ba Mai ya yaba wa Gwamna Farfesa Baba Gana Zulum bisa jajircewarsa wajen ƙarfafa wa ’yan jihar da kuma mambobin ƙungiyarsa da motocin sufuri, inda ya buƙaci mambobinsa da su ci gaba da tallafa wa gwamnati don samar da romon dimukuraɗiyya ga jama’a.
Alhaji Ba Mai ya ce baya ga shirin tallafa wa mambobinsa su yi amfani da tsarin manufofin gwamnati wajen samar da ababen hawa da motocin bas ga ƙungiyar ga gwamnati.
Shugaban ƙungiyar na NURTW reshen Bama, ya shawarci matasa da su zama jakadun ƙasa nagari, su guji shan miyagun ƙwayoyi, su kuma saurari shawarwarin iyayensu a koda yaushe, su bai wa neman ilimi da sana’o’i muhimmanci.
Ba Mai ya kuma yaba wa Gwamna Farfesa Baba Gana Zulum a fannin samar da ingantattun tsarin kiwon lafiya ta hanyar gina cibiyoyin kula da lafiya da kuma ayyuka a ƙananan hukumomi 27 na jihar, inda ya buƙaci mambobinsa da su ci gajiyar shirin inshorar lafiya a jihar.
Ba Mai ya yi amfani da wannan damar wajen miƙa ta’aziyya ga gwamnatin tarayya, gwamnatin jihar Borno, Shehun Borno, Shehu Garbai Elkanami bisa ibtila’in ambaliyar riwa a Jere kwanakin baya. Ya yi kira ga masu hannu da shuni da ƙungiyar haɗin kai da su tallafawa waɗanda ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu a Maiduguri.
Kazalika ya yaba da nasarorin da aka samu na kafa Hukumar Cigaban Arewa Maso Gabas (NEDC), ya buƙaci hukumar da ta yi la’akari da mambobinsa ta hanyar samar da shirin aiki don mambobinta su ci gajiyarsu. Ya yaba da nasarorin da hukumar ta samu a ayyukan ci gaban al’umma.
Ba Mai Mustapha, ya yaba da salon jagorancin Mataimakin Shugaban ƙasa Sanata Kashim Shettima da yake jagorantar ayyukan hukumar raya yankin arewa maso gabas, ya kuma ce da kafa ma’aikatar raya yankin ya kamata a bar mai kula da ma’aikatar a ƙarƙashin ofishin mataimakin shugaban ƙasa.
Ya buƙaci mambobinsa da su kasance masu bin doka da oda ta hanyar biyan haraji don tallafa wa gwamnati wajen ƙara ƙaimi ga ci gaban jihar baki ɗaya, kuma su kasance masu haƙuri a koyaushe.
Ba Mai ya buƙaci mambobin ƙungiyar da su mara wa shugaban ƙungiyar na jiha Alhaji Abba Shuwa da dukiyar ƙasa goyon baya.