Daga HABU DAN SARKI a Jos
Shugaban Jam’iyyar PDP na ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa, Alhaji Aminu Abdullahi, ya yaba wa sabon Kansilan Unguwar Abba Na Shehu, Auwal Hassan Tubarkallah, sakamakon yadda ya nuna kyakkyawan misali ga sauran sabbin zaɓaɓɓun ‘yan siyasa da ba a jima da zaɓen su ba a Jihar Filato, musamman dangane da aikin rabon ruwa da ya ɗauki nauyi a dukkan sassan unguwar, biyo bayan halin da jama’a suka shiga na ƙuncin rashin ruwa a makonnin nan, wanda ke da nasaba da katsewar wutar lantarki da aka fuskanta a wasu jihohin arewacin Nijeriya.
Shugaban ya ce, idan har shugabanni da wakilan al’umma a dukkan matakai za su riƙa yin irin haka, domin sauƙaƙawa jama’ar da suke wakilta, babu shakka talakawa za su ji daɗin rayuwa, kuma ba za a shiga irin ƙuncin da ake fuskanta a yanzu ba. Yayin da ya ƙara tunatar da sauran ‘yan siyasa su riƙa tunawa da alƙawuran da suke yi wa jama’ar su a lokacin yaƙin neman zaɓe, domin watarana za su sake komawa wajen su neman ƙuri’a. Sannan kuma Ubangiji zai yi musu hisabi kan amanar talakawa.
“Mun ji daɗi, mun yi murna, mun yi farinciki sosai da wannan taimako da Kansilan mu ya kawo. Ya ƙara mana ƙwarin gwiwa, ya kuma nuna mana shi ma’aikaci ne, tabbas ba mu yi zaɓen tumun dare ba. Gaskiya muna alfahari da wannan abin da Tubarkallah ya yi!”
Shi ma shugaban ƙungiyar matasan unguwar Abba Na Shehu, Mubarak Abubakar wanda aka fi kira da Washa, ya tabbatar da wannan aikin rabon ruwa da aka yi, tare da jaddada farincikinsa a madadin sauran mazauna unguwar Abba Na Shehu, waɗanda ya ce a kwanakin da aka yi babu wutar lantarki, da ake amfani da ita wajen kunna ruwan bohol da ake sayarwa a Unguwar, jama’a da dama sun shiga ƙunci da wahala. Amma sai gashi wannan Kansila da ko wata guda bai yi da samun matsayin nan ba ya kawo wa al’ummar unguwar sa sauƙi a halin da suke ciki.
Ya yi fatan wannan Kansila zai cigaba da yin ayyukan alheri ga jama’ar Abba Na Shehu, kamar yadda yanzu ya fara muna cewa shi mai yi ne, kuma mutane ba za su yi nadamar zaɓar sa da suka yi ba.
Da yake zantawa da manema labarai, sabon Kansilan Abba Na Shehu, Auwal Hassan Tubarkallah, ya yi godiya da goyon baya da amincewar da jama’ar Abba Na Shehu suka bashi wajen zaɓen sa da suka yi, tare da alƙawarin samar musu ayyukan cigaba da za su inganta rayuwarsu da ta iyalinsu.
Ya kuma bayyana cewa, ya ɗauki nauyin samar da wannan ruwa ne a shiyyoyi uku na Abba Na Shehu, domin lura da ya yi da halin da jama’a ke ciki, sakamakon katsewar wutar lantarki. Don haka ya yi amfani da kuɗaɗen aljihunsa don rage raɗaɗin da jama’a ke fama da shi, kafin al’amura su dawo daidai.
“In sha Allahu, ina da tsare-tsare da dama da nake son idan na samu dama zan gudanar da su domin al’umma su ji daɗi. Yanzu haka ba ƙaramin kuɗi na kashe ba, wajen sayen motar ruwa, da sayen man fetur da aka sa a injunan tayar da bohol don samar da ruwa a ɓangaren Abba Na Shehu A, B, da C. Kuma, da izinin Allah, wannan masomi ne, don yanzu muka fara.”
