An yi jana’izar ɗan uwan Gwamna Tambuwal, Muhammadu Bello

Daga WAKILINMU

An gudanar da jana’izar babban yayan Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sakkwato, wato Muhammadu Bello (Wazirin Tambuwal).

Marigayi Muhammadu Bello ya rasu ne da yammacin jiya Talata

Tun farko MANHAJA ta rawaito cewa sanarwar rasuwar ta fito ne ta hannun ƙanin marigayin kuma gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal (Mutawallen Sakkwato).

Sanarwar ta nuna Marigayin ya shafe shekaru 37 riƙe da muƙamin Wazirin Tambuwal tun bayan da ya gaji mahaifinsu, Alhaji Umar Waziri Usmanu.

Taron jana’izar ya samu halarcin ‘yan uwa da masoya na kusa da nesa.