‘Yan Kannywwod sun karrama A.A. Zaura

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano

Ƙungiyar jarumai masu shirya fim da masu waƙa a masana’antar Kannywwod, wato ‘Kannywwod Celebrity Forum’, sun shirya wani taro domin karrama gwaninsu a fagen siyasar Jihar Kano, wato Alhaji Abdussalam Abdulkareem, wanda aka fi sani da A. A. Zaura.

Taron, wanda a ka gudanar da shi a ranar Asabar ɗin da ta gabata, ya samu halartar matasa da kuma dattawa na cikin masarautar ta Kannywwod.

Fitaccen jarumi, mawaƙi kuma furodusa T. Y. Shaba, shi ne jagoran shirya taron, inda a cikin jawabin sa ya ce, “sun shirya wannan taron ne domin su karrama A. A. Zaura bisa cancantar sa da kuma hidimtawa jama’a musamman a ɓangaren addinin Muslunci da sauran ɓangarorin rayuwa na yau da kullum da kuma kasancewar sa ɗan siyasa a Arewa da ya fi kowanne halin dattako da karamci.”

Shi ma a na sa jawabin jigo a masana’antar Kannywwod Mai Unguwar Mandawari Alhaji Ibrahim Mandawari, ya yaba wa A.A Zaura bisa ayyukan da yake yi na jin ƙai da kuma taimakon jama’a, sannan da gudunmawar da yake bai wa masarautar ta su mai ɗimbun tarihi.

Ya ƙara da cewa, “Mu na da ɗimbin gudunmawar da za mu bayar don ganin an kafa sabuwar Jihar Kano, kuma za mu yi bakin-ƙoƙarin mu don ganin an samar da cigaba a Jihar Kano da ma ƙasa bakiɗaya.”

Shi kuma a na sa jawabin A.A Zaura, ya nuna godiyar sa da karramawar da ‘yan fim suka yi masa, saboda abin alfahari ne da zavo shi da suka yi a cikin ‘yan siyasa saboda ganin da suka yi masa a matsayin wanda zai kawo cigaba a Jihar Kano.

Daga ƙarshe ya yi kira ga ‘yan fim da su mayar da hankali a sana’ar ta su wajen wayar da kan mutane musamman a kan illar shaye shaye da lalacewar tarbiyya a cikin finafinan na su. “