An yi walimar taya sakataren dindindin na ma’aikatar ilimin Jihar Kano, Bashir Baffa murna

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

An bayyana Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf da cewa babu wani abu da ya fiifita a gabansa da ya wuce harkar bunƙasa ci gaban ilimi, ta bijiro da tsare-tsare na cigaban ilimi  amma sai an yi haƙuri abubuwa za su tafi yadda ake so sakamakon irin matsalolin da suka zo suka samu a harkar ilimi.

Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano Hon. Haruna Doguwa ne ya bayyana hakan a yayin taron walima da ƙungiyar shugabannin makarantun sakandire suka shiryawa sabon sakataren dindindin na ma’aikatar ilimi na jihar Kano Kwamared Bashir Baffa Muhammad.

Ya ce zuwan su gwamnati sun taras da harkar ilmi a wani mawuyacin hali wataƙila da dama- dama a makarantun sakandire, amma a makarantun furamare  wasu wuraren idan kaje  duk mai son cigaban ilimi sai ya zubar da hawaye.

Ya ƙara da cewa hatta kuɗin jarrabawar makarantun Arabiyya na ‘yan shekarar 2021 da 22 da 23 ba a biya ba,  tana riƙe a wajen hukuma ma’anan wannan shine idan akwai yaro da yayi jarabawar ƙarshe ta makarantar Arabiyya a Kano  wani da ya yi a jihar Jigawa  shi na Jigawa yana mataki na Biyu ko na Uku a jami’a amma na Kano na gida bai ma karɓi sakamakon jarabawar ba sai zuwan Abba aka biya.

Ya ce sun samu makarantun guda firamare a Kano ta Arewa guda 300 gaba ɗayansu malami ɗaya ne a kowanensu, abubuwa na taƙaici da jin haushi da suka gani lokacin da ya zo yana zagaye a Kwalejin Fasaha ta ƙofar Nasarawa ɗakin  gwaje-gwaje na kwalejin wani ya mayar ban ɗakinsa wannan na daga irin lalacewar da suka sami ilimi a ciki.

Doguwa ya ce da su da malaman makarantu da Gwamnan Kano aiki ne me nauyi na a kansu  yadda za su gyara ilimin jihar Kano aikin yana da wahala musamman ga shugabannin makarantu duk wanda yake makarantar kwana shaida ne akwai lokacin da a baya shugabannin makarantun ne ke haɗa kuɗi su ciyar da ɗaliban, amma yanzu wannan ya kau abubuwa na gyarawa.

Ya ce yanzu an wadata makarantu da kayan aiki kuma ana tsare -tsare na baiwa malamai guda 1000 bashi yanzu akwai kayan ɗakin gwaje gwaje guda 300 da Gwamna ya samar da za a raba makarantu duk abinda ake ana yi ne domin gyara ilimi a jihar Kano.

Ya ja hankalin shugabannin makarantu da cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na sane da halin da suke ciki na kuɗaɗen gudanarwa na makarantun su kuma komai ya kusa tabbata kuma suna godiya ga Allah bisa matakai da ake ɗauka hakan tasa a  bana  jahar Kano ta zama ta biyu a cin jarabawar da ɗalibai suka yi.

Haruna Doguwa ya ce suna ta ya sabon sakataren na dindindin a ma’aikatar ilimi Kwamared Bashir Baffa murna kuma da yardar Allah za a yi aiki na ciyar da jihar Kano gaba.

Shi ma a nasa jawabin Alhaji Bashir Baffa Muhammad  da aka shirya walimar domin taya shi   murnar ya ce yana neman a ta ya shi da  addu’ar Allah ya sa ya sami daman taimakawa cigaban ilimi a Kano.

Kwamared Baffa Muhammad  ya ce abinda yake soma a sani Allah ya haɗa shi da waɗanda suka so ya koyi aiki,shi kansa  Kwamishina ya same shi  aikin da babban sakataren dindindin  yake kusan  shi yake koya masa, kuma ya zo ya sami Kwamishina da ya fishi ƙaunar ya ga cigaban ilimi.

Sakataren na dindindin Bashir Baffa  Muhammad ya ce abinda ya fahimta da zama da  Kwamishina Haruna Doguwa shine gaba ɗaya ƙudirin da Gwamna yake so ya gudanar a jihar Kano shima ya hau kai ,kuma shima  yana sa shi a tafarkin,  al’umma data taru don ta ya shi murna ya nuna Gwamnati ta na kan tafarki.Bayanin da Gwamnan Kano Abba Kabir  yake na a dafawa ilimi, muhimman mutane da dama da ya ga irin fuskokinsu ya nuna ana amsa kiran  gwamnati na dafawa ilimi.

Shi ma a jawabinsa ga yan jarida Malam  Abdulkarim Ibrahim  Abubakar shugaban  kwalejin nazarin ƙur’ni na Abdullahi Bayero ɗaya daga waɗanda suka shirya walimar ya ce sun shirya ne domin ta ya sabon sakataren na dindindin na ma’aikatar ilimi Bashir Baffa Muhammad  murna  a matsayinsa na ɗaya daga cikinsu 

Malam Abdulkarim Ibrahim ya  ce  Bashir Baffa Muhammad  mutum ne shi na mutane mai son jama’a da karamci da alkhairi da sauƙin kai duk da  wannan babban  mukami da ya samu kullum yana nuna kansa a matsayin daidai  suke da shi  dan haka  za su bashi haɗin kai da goyon baya don cimma nasara.