Dalilan da ya sa mahaifina ya auri mata 30 da ‘ya’ya 108 – Gwamnan Ebonyi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya bayyana dalilan da suka sa mahaifinsa, Ezekiel Nwifuru, ya auri mata har 30 da kuma haihuwar ‘ya’ya 108.

Nwifuru ya bayyana hakan ne a ƙarshen mako a lokacin bikin naɗa mahaifinsa Sarkin Oferekpe Agbaja kamar yadda jaridar Sun ta rawaito.

Ezekiel da fari ya auri mata 30 ne, sai dai izuwa yanzu adadinsu ya dawo 29 saboda goge sunan wasu daga jerin matansa sakamakon gaza haihuwa da suka yi.

Sannan matan nasa 19 su ne suka haifa masa ‘ya’ya 108 amma bayan naɗa shi wannan sarauta, a yanzu matansa 17.

Sannan an samar da masarautar wacce ke da ƙauyuka 17 bayan wata doka da aka gabatar wa da majalisar dokokin jihar da kuma ta amince da ita.

Nwifuru ya bayyana cewa mahaifinsa mai shekaru 84 ya zama attajiri ne sakamakon aiki tuƙuru da ya yi a matsayinsa na manomi wanda ya jawo masa hassada da barazana daga al’ummar yankin na Agbaja. Ga kuma cin mutunci da ya sha daga ‘yan uwansa da maƙwabta.

Ya ce bambancin da wulaƙancin da ya sha a hannun al’umma ne ya sanya shi auren mata da yawa domin su zame masa abokai da kuma kai wa ga cikar burinsa.

Nwifuruya buƙaci mahaifinsa da ya yi amfani da kujerarsa wajen bunasa zaman lafiya da adalci da a cikin al’umma tare da shawartarsa da ka da ya ɗauki fansa kan waɗanda suka gallaza masa.

“Ka da ka yi amfani da matsayin wajen ɗaukar fansa da rashin adalci. Kamata yi ka yi amfani da muƙamin a matsayin ‘yar manuniya na adalci da haɗin kai da hidimta wa al’umma,” a cewar gwamnan ga mahaifinsa.