Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wasu malamai sun koka akan Gwamnatin Tarayya, domin sanya hannu akan yarjejeniyar
nan mai cece-kuce ta Samoa, wacce ake zargin ta na ƙunshe da amincewa da tsarin auren
jinsi.
A cewarsu, yarjejeniyar tana ɗauke da wasu sharaɗai da suka ƙunshi cewa ƙasashe masu
tasowa dole su yarda da ’yancin ’yan luwadi da ’yan maɗigo da kuma ’yancin yin auren jinsi
ɗaya.
Yarjejeniyar an samar da ita a tsibirin Samoa, inda aka sanya ma ta hannu a ranar 15 ga
Nuwamba, 2023, amma tun lokacin yarjejeniyar ke samun suka daga addinai da dama,
saboda hakan ya saɓa wa addininsu da al’adunsu.
Bayanai akan yarjejeniyar ya fito ne lokacin da Ministan Kasafin Kuɗi Da Tattalin Arziki, Alhaji
Abubakar Atiku Bagudu, ya bayyana irin halin da ake samu, a wata liyafa da Ƙungiyar
Ƙasashen Turai suka shirya a Abuja. Duk da dai ya ce, Nijeriya ta sa hannu ne a sashin bashin
Dala biliyan 150.
Ƙasashe da dama a duniya sun ƙi yarda sun sanya hannu kan yarjejeniyar a 2023 lokacin da
aka yi ta. Ƙasashen sun haɗa da Guinea, Trinidad and Tobago, Mauritania da wasu ƙasashen
Afirka da dama.
Yanzu haka wannan lamari ya jawo cece-kuce a shafukan sada zumunta na Nijeriya, inda
’yan Nijeriya ke nuna allawadai da wannan lamarin.
Duk ƙoƙarin da Blueprint Manhaja ta yi na jin ta bakin Gwamnatin Tarayya kan lamarin, don
jin ƙarn bayani ya ci tura, domin Mai Magana da Fadar Shugaban Ƙasa, Abdul’aziz
Abdul’azil, bai amsa kiran da mu ka yi masa ba kuma har zuwa lokacin wallafa wannan
rahoton bai kira ba.
