Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta umarci alƙalan babbar kotun jihar, Mai Shari’a Faruk Lawal Adamu da Mai Shari’a Zuwaira Yusuf, wa’adin awa 48 su sauka daga shugabancin kwamitocin binciken da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kafa domin bincikar tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje.
Alƙalan biyu ne ke jagorantar kwamitoci biyu da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kafa don bincikar Gwamnatin Ganduje kan zargin karkatar da kuɗaɗe da kadarorin gwamnati da kuma kwamitin bincike kan rikicin siyasa da ɓacewar mutane daga 2015 zuwa 2023.
Mai Shari’a Simon Amobeda, ya umarci Hukumar Kula da Harkokin Shari’a ta Ƙasa (NJC) ta tsayar da alabshi da duk da sauran hakkokin alƙalan biyu, muddin suka saba umarnin kotun.
Ya sanar da haka ne a lokacin da yake yanke hukuncin kan ƙarar da Ganduje ya shigar gaban kotun.
Ya bayyana cewa Gwamna Abba ba shi da hurumin naɗa alƙalai domin gudanar da aikin ɓangaren zartarwa.
Ya kuma umarci alƙalan da su daina shiga aikin bangaren zartarwa da gwamnan ya ba su, alhali suna sanye da rigarɓa alƙalanci da yanke hukunci tsakanin bangarorin da ke da sabani da juna a jihar.
“Kundin Tsarin Mulki bai halasta wa wadanda ake kara, Mai Shari’a Faruk Adamu da Mai Shari’a Zuwaira Yusuf waɗanda alƙalan Babban Kotun Jihar Kano ne, su karbi mukamin shugabancin kwamitin bincike ba, wanda daidai yake da matsayin alkalin kotun Majiatare,” in ji shi.
Ya ci gaba da cewa Gwamna Abba ba shi da hurumin nada wa da kuma rantsar da alkalai domin su gudanar da aiki shugabannin kwamitocin bincike, wanda aiki ne da doka ta ba wa Kwamishinoni da ke bangaren zartarwa.
Ya ce la’akari da hukuncin da Mai Shari’a Abdullahi Muhammad Liman ya yanke cewa hukumar EFCC da ICPC ne kaɗai za su iya bincikar tsohon gwamna, raina kotu ne da wuce gona da iri abin Gwamna Abba ya yi na neman bincikar Ganduje, alhali gwamnatin jihar ba ta daukaka kara a kai ba kuma kotun ɗaukaka ƙara ba ta jingine hukuncin ba.
