Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
An bayyana Gwamnan Jihar Kan, .Alhaji Abba Kabir Yusuf da cewa mutum ne mai tausayi da
imani duk lokacin da aka ce wata matsala ta shafi al;umma ba wai ;yan kasuwar kaɗai ba zai
zauna ya samu sukuni ba sai ya tabbatar ya warware matsalar.
Hon. Alhaji Isa Wise, Babban Mataimaki na biyu ga Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir
Yusuf kan harkokin kasuwanci ne ya shaida hakan ga yan jarida.
Ya ce dalilin da ya sa aka cire teburan yan kasuwar a kewayen filin Idi shine don samar da
sarari lokacin sallar idi domin mutane ya zama sun yi Sallah cikin kwanciyar hankali ababen
hawa su sami shiga da fita cikin kwanciyar hankali da walwalla ba tare da takura ba.
Ya ce an yi wannan tsarin amma saboda rashin fahimta gabatarwa wannan abin ya sa
mutane suka tada hankalinsu suke ganin kamar korar za a yi. Amma da kuka ya yi yawa
Gwamna ya ce shi yana tare da da al;ummar Kano da ;yan kasuwa yasan irin gudunmawa da
suka bashi.
Hon Isa Wise ya ƙara da cewa Gwamna ya ce kashi 75 na;yan kasuwa da suke harkoki a
kewayen masallacin idi kan titin IBB masoya ne da suka taimaki tsarin kKwankwasiyya don
haka aje a gaggauta a yi tsari cikin mutuntawa da daraja yadda kowa zai cigaba da sanaarsa
a wajen bisa kiyaye doka.
Ya ce har ma Gwamna ya yi wa shugabannin yan kasuwar waɗanda suka je gidan Gwamnati
suka koka masa tagomashi na kuɗi N50,000 kowannen su sun kuma yaba da gamsuwa
Gwamna Abba Kabir Yusuf adali ne mai saurare da son cigaban alumma.
Ya ƙara da bayanin cewa da akaje gaban Gwamna akan alamarin yan kasuwar na IBB
abinda ya soma dubawa shine wasu da suke maganar wajen akwai yan adawa na wata
jamiyyar daban amma ya ce shi duk ɗan jihar Kano nasa ne, ba maganar ɗan kaza ko ɗan
kaza duk mai haƙƙi a wajen a mayar masa.
Hon Isa Wise ya ce yanzu an wayi gari waɗanda ke wata jamiyyar ma sun ci alwashin idan
zaɓe ya zo ƙuri;arsu ta Abba Kabir Yusuf ce sakamakon abin alkhairi da kulawa da ya yi
musu.
