Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar shirya jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta ƙasa (JAMB) a Nijeriya ta bankaɗo daliban da suka kammala karatun jamia na bogi 3,000 da kuma mallakar takardun shaidar kammala karatu ba bisa ƙaida ba a duk faɗin ƙasar.
Magatakardar hukumar, Farfesa Ishaƙ Oloyede ne ya bayyana hakan kuma ya ce waɗannan mutane ba su taɓa zuwa jami’a ba, wanda hakan ya nuna irin cin hanci da rashawa da ake samu a harkar ilimi.
Oloyede ya soki yadda wasu cibiyoyin karatu suke shigar da ɗalibai makarantu ba bisa ƙa’ida ba, yana mai cewa abin kunya ne ga al’ummar ƙasar. Ya kuma buƙaci kwamitin Pro-Chancellor na Jami’o’in Jihohi a Nijeriya (COPSUN) da su yaƙi irin waɗannan ayyuka.
A watan Disamban 2023, Kwamitin Majalisar Wakilai kan Ilimin Farko ya buƙaci Hukumar JAMB ta samar da jerin sunayen cibiyoyin da ke da hannu wajen shigar da ɗaliban jamioi ba bisa ƙa’ida ba. A shekarar da ta gabata ne kuma JAMB ta ba da shawarwari kan hanyoyin da za a bi don gano yadda ake shigar da mutane jamioi ba bisa ƙaida ba.
Tun da farko dai hukumar jarabawar ta gargaɗi masu neman gurbin karatu da su daina karɓar damar samun karatu da irin waɗannan cibiyoyi ke yi ba tare da cikakken halartar jarabawa da ƙaidojin shiga jamia ba.
Hukumar JAMB ta kuma mayar da martani ga ƙorafin da aka yi a kafafen sada zumunta game da tsarin daidaita jarabawa, inda ta ce dole ne duk waɗanda suka rubuta jarabawar su bi ta JAMB domin kaucewa kura-kurai.Oloyede ya lura cewa daga shekarar 2017 zuwa 2020, cibiyoyin karatu a Nijeriya sun gudanar da shigar da sama da ɗalibai 706,000 jamioi ba bisa ƙaida ba, da gurɓata kididdigar rajista na ƙasa da kuma karya manufofin ilimi.
