’Yan ƙwadago sun yi tir da sabon ƙarin kuɗin lantarki

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyoyin Ƙwadagon Nijeriya NLC da TUC, da kuma ƙungiyoyi masu zaman kansu sun soki ƙarin kuɗin wutar lantarki ga kwastomomi masu layin Band A. Kamfanonin rarraba wutar lantarki da dama da suka haɗa da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Ibadan, Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Eko, da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kaduna, sun sanar da cewa farashin kwastomomi na layin Band A zai tashi daga Naira 206.80 a kowace kilowatt zuwa Naira 209.50. Wannan ƙarin da Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Nijeriya ta aiwatar, na da nasaba da faɗuwar darajar Naira a kan Dalar Amurka da hauhawar farashin kayayyaki da dai sauransu.

Duk da cewa an samu ƙaruwar da ake ganin zai kawo sauyi, ƙungiyoyin ƙwadago, masu zaman kansu, da masu saye da sayarwa sun bayyana rashin amincewarsu da matakin.Sun yi mamakin dalilin da ya sa hukumar kula da samar da wutar lantarki za ta amince da ƙarin kuɗin, duk da kiraye-kirayen da aka yi na a sauya yadda kae yawan ƙarin kuɗin lantarki.

Mataimakin shugaban ƙungiyar masu ƙananan masana’antu ta Nijeriya, Segun Kuti-George,ya ce matakin zai haifar da ƙarin rufe masana’antu“Ba ma buƙatar wani ƙarin kuɗi a yanzu. Duk wani haɓakar abubuwan da aka shigar zai fassara zuwa haɓakar farashi. Mun riga mun sami ƙaruwar farashi, wanda ke nufin muna fuskantar ƙaruwar farashin masanaantu. Wannan baya dorewa.

“Ƙarin farashi akai-akai zai haifar da raguwar buƙatun kayayyakin da ake ƙerawa a cikin gida, wanda hakan zai sa su kasa yin gogayya da kayayyakin da ake shigowa da su daga China. Wannan zai haifar da raguwar riba, wanda zai iya haifar da ƙarancin masanaantu.

Idan har masana’antu ba za su iya sayar da kayayyakinsu ba, za su iya yin amfani da damar rage albashi ko korar ma’aikata, wanda hakan na iya haifar da ƙaruwar laifuka. “Tare da hauhawar farashin kayayyaki sama da kashi 30 cikin 100 da kuma ribar rancen banki a kashi mai yawa, ya kamata mu yi la’akari da hanyoyin da za mu tallafa wa kayayyakin da ake kerawa a cikin gida domin kara yin gasa. Maimakon haka, muna ƙara farashi, yana sa ya yi wuya masanaantu su rayu. Wannan abin takaici ne, musamman idan muka ga wasu ƙasashe irin su Jamhuriya suna ba da wutar lantarki a farashi mai rahusa.”Kuti-George ya ce, ya kamata a sassauta harkar wutar lantarki don ba da damar yin gasa irin ta na’urorin sadarwa don rage tsadar kayayyaki da kuma inganta ayyuka.

By ukarofi