Ana yi wa ƙasurgumin ɗan bindiga caffa a Katsina bayan zaman kurkuku a Nijar

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

An saki Kachallah Bammi Yarma, ƙasurgumin ɗan bindiga da hukumonin ƙasar Nijar suka yanke wa hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekara 9 tun shekara ta 2015, bayan da aka yanke masa hukuncin kisa.

A halin yanzu ƙasurgumin ɗan bindigar ya dawo yankin Jihar Katsina da ke Nijeriya, lamarin da ya jefa tsoro da fargaba a zukatan al’umma duba da cewa, Yarma ya yi ƙaurin suna wajen yin garkuwa da mutane, satar shanu gami da safarar makamai.

Zagazola Makama, fitaccen mai bincike kan aikace-aikacen ‘yan ta’adda kuma mai sharhi kan lamauran tsaro, ya tabbar da sakin ɗan bindigar a shafinsa na sada zumunta, inda Makama ya bayyana cewar, Yarma ya koma yankin Jihar Katsina da zama har ma manyan ‘yan bindinga sun fara tallafa masa da makamai don cigaba da ayyukansa na satar mutane domin neman kuɗin fansa.

Bammi Yarma, wanda ya yi suna wajen ta’addanci da kashe-kashe, an kama shi ne a shekarar 2015 a zamanin tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari.

An kama shi ne a lokacin da yake yunƙurin safarar makamai saman rakuma guda tara da aka loda wa bindigogi a garin ɗanmusa na jihar Katsina.

“A lokacin da aka cafke shi, hukumomi sun kama shanu da wasu dabbobi 1,000 na sata, kamen ya kawo cikas ga wata babbar hanyar samar da makamai ga ‘yan fashin daji,” inji wata majiyar leƙen asiri.

Daga nan ne aka yanke wa Bammi Yarma hukuncin ɗauri a Jamhuriyar Nijar saboda rawar da ya taka a harkar ta’addanci.

Sai dai yanzu haka wasu majiyoyi na leƙen asiri sun tabbatar da sake bayyanar ɗan bindigar a yankin Arewa maso yammacin ƙasar, lamarin da ya haifar da fargabar tasirin dawowarsa.

Rahotanni sun bayyana cewa shugabannin ‘yan bindiga daga daban-daban na yin mubaya’a ga Bammi Yarma, inda kowanensu ke ba shi kyautar makamai da suka haɗa da bindigogi daga biyar zuwa goma don muryar sakinsa.

Laifukan da Bammi Yarma ke aikatawa sun haɗa da kai munanan hare-hare, garkuwa da mutane da kuma satar shanu a wasu jihohin arewa.

Shaharar sunansa ya wuce iyakokin Nijeriya, inda rahotanni ke nuna cewa hatta ƙungiyoyin ‘yan ta’adda a Nijar da yankin Sahel na fargabar tasirinsa duba da yadda ake alaƙantasa da kashe wasu shugabannin ‘yan bindinga irinsu Kachalla Kundu da baya jituwa da su.

By ukarofi