APC ce za ta lashe zaɓen ƙananan hukumomi a Jihar Kaduna – Uba Sani

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Yayin da ake cigaba da shirye-shiryen gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomi a jihar Kaduna, Gwamna Uba Sani ya yi kurin cewa jam’iyyarsa ta APC ce za ta lashe kujerun shugabannin ƙananan hukumomi da na kansiloli kaf ɗinsu.

Gwamna Sani ya bayyana haka ne a makon jiya yayin da yake miƙa wa ‘yan takarar jam’iyyar na APC tuta.

Taron ya samu halartar gaggan jam’iyyar APC, da magoya baya daga duka ƙananan hukumomin jihar.

Yayin da yake jawabi gwamna Sani ya ce jam’iyyar APC ce jam’iyya ɗaya tilo a jihar Kaduna yanzu. Babu wata jam’iyya da za ta taɓuka wani abu a zaɓen ƙananan hukumomi da za a yi ranar 19 ga Oktoba.

”Babu wata jam’iyya a jihar Kaduna sai APC, kuma ita ce za ta lashe duka kujerun shugabannin ƙananan hukumomi, da na Kansiloli kaf ɗin su. Kuma ku je ku ce na faɗi.

Gwamna Sani ya ƙara da cewa yana goyon bayan maida wa ƙananan hukumi cikakken iko da basu damar kashe kuɗaɗen su kai tsaye ba tare da gwamnoni sna yi musu katsalandan ba.

Zaɓen ƙananan hukumomi dai ya zamo tuwo ma mai na ne a jihohin ƙasar nan, inda jam’iyyar da ke mulki, ita ce ke cinye kujerun kaf.

Sau da yawa akan riƙa yi wa jam’iyyar adawa shaguɓe cewa kada ma su kashe kuɗaɗen su wajen yin kamfen.

By ukarofi