An zaɓi Palmer a matsayin gwarzon ɗan wasan Ingila na 2023-24

Spread the love

An bayyana Cole Palmer a matsayin gwarzon ɗan wasan ƙwallon ƙafar maza na Ingila a kakar wasa ta shekarar 2023-24.

ɗan wasan, wanda  magoya bayan ƙwallon ƙafa su ka zaɓa, ya shige gaban Jude Bellingham da Bukayo Saka, waɗanda su ka kammala a matsayi na biyu da na uku.

A watan Nuwamban shekarar da ta gabata ne Palmer ya fara buga wa tawagar ƙwallon ƙafar Ingila wasa, da wasan da Ingila ta doke Malta da ci 2 da nema a filin wasa na Wembly.

Sau tara ya buga wa ƙasarsa wasa, kuma daga cikin wasanni taran, guda biyu ne kawai aka fara da shi, kana wasanni biyar daga cikin taran, ya buga su a gasar Euro 2024, inda ya ci ƙwallo a wasan ƙarshe da Ingila ta fafata da Sifaniya, wanda aka doke ta 2-1.

Zaɓen nasa na zuwa ne bayan da aka bayyana shi a matsayin gwarzon matashin ɗan wasa na gasar Firmiyar Ingila a watan Agusta, biyo bayan bajintarsa a Chelsea.

Haka zalika, ɗan wasan gaba na ƙungiyar Arsenal Bukayo Saka, ya taya abokin wasansa a tawagar Ingila Cole Palmer murnar lashe kyautar gwarzon ɗan wasan ƙasar na bana.

Cole Palmer ya samu nasarar ce bayan da ya shiga gaban Saka da kuma Jude Bellingham.

Ina taya Cole murnar lashe wannan kyautar, babbar nasara ce kuma ya can-canci hakan, ina zaune kusa da shi lokacin da aka sanar da shi ne ya lashe wannan kyauta, ya kasa rufe bakinsa domin bai taɓa zaton hakan zata faru ba.

Duk da cewa babu wasa ko guda da aka fara da Palmer a gasar Euro da Jamus ta karɓi baƙunci a bana, amma ya taimaka wa tawagar ta Ingila wajen kaiwa ga wasan ƙarshe, musamman ƙwallo da ya taimaka aka ci Netherland a wasan kusa dana ƙarshe.

Haka nan Palmer ya kuma ci ƙwallonsa ta farko a tawagar Ingila, a wasan ƙarshe na gasar Euro da suka sha kashi a hannun Sifaniya da ci 2-1.

By ukarofi