APC: Ra’ayin Tinubu kan murabus ɗin Ganduje da batun sauya sheƙar Kwankwaso

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Jam’iyyar APC ta tabbatar da cewa tana gudanar da shawarwari game da batun maye gurbin tsohon shugabanta, Abdullahi Ganduje, wanda ya yi murabus a makon da ya gabata.

Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar, Feliɗ Morka a wata hira da gidan telebijin na ‘Channels’, ya ce APC tana aiki da lissafi wajen ganin ta cike gurbin da ganduje ya bari.

Ya kuma ce, za a sanar da sabon shugaban jam’iyyar ne a yayin gudanar da babban zamanta na ƙasa, wanda kawo yanzu ba a bayyana ranar da za a yi haka ba.

Game da batun yiwuwar tsohon gwamnan Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso ya dawo APC daga jam’iyyar NNPP, Morka ya ce zuwa yanzu babu wata tattaunawa ta musamman akan haka.

Morka ya kuma yi watsi da raɗe-raɗen da ake yaɗawa da ke cewa akwai wasu matsalolin cikin gida da ke hana ruwa gudu a yayin gudanar da harkokin jam’iyyar.

A yayin tambayar cewa ko ƙila Shugaba Tinubu yana fushi da Ganduje akan ajiye muƙamin nasa, Sakataren ya ce waɗannan kalamai jita-jita ne marasa asali.

A ranar 27 ga watan Yuni ne Morka ya sanar da batun murabus ɗin da Ganduje ya yi daga jagorancin jam’iyyar a mataki na ƙasa, lamarin da ya ce ya faru ne sakamakon matsalolin gaggawa da suka shafi lafiyarsa.

Bayan haka ne Shugaba Tinubu ya umarci a naɗa Mataimakin Shugaban jam’iyyar na Arewa, Ali Bukar Dalori a matsayin Shugaban riƙon ƙwarya har zuwa lokacin zaman Majalisar Zartarwar jam’iyyar (NEC), inda za a zaɓi na dindindin.

Ganduje, wanda ya fito daga yankin Arewa maso Yamma, ya karɓi muƙamin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa ne a watan Agustan 2023, biyo bayan murabus din da magabacinsa, Abdullahi Adamu, ya yi daga shiyyar Arewa ta tsakiya. Wa’adinsa ya ci karo da suka daga wasu ɓangarori na jam’iyyar da suka yi imanin naɗin nasa ya saɓa wa tsarin shiyyar cikin gida.

Gwamna Ganduje wanda ya yi wa’adi biyu a jihar Kano (2015–2023), an naɗa Ganduje a matsayin shugaban hukumar kula da filayen jiragen sama ta Nijeriya (FAAN) a watan Janairun 2025. Har ila yau, an ce an ɗauke shi a matsayin jakadan da ba na aiki ba.

By ukarofi