Majalisar Ayyukan Shari’a ta ƙasa ta kori alƙalai 10

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Majalisar Kula da Harkokin Shari’a ta ƙasa (NJC) ta kori wasu alƙalai 10 a jihar Imo bisa laifin ƙara shekaru da kuma aikata wasu munanan ɗabi’u.

Wannan shawarar ta biyo bayan taron majalisar karo na 109 da ta gudanar a Abuja wanda Babbar Mai Shari’a ta Nijeriya (CJN), Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun ta jagoranta.

A wata sanarwa da majalisar ta fitar a ranar Alhamis, ta bayyana cewa alƙalan da abin ya shafa da suka haɗa da biyar daga babbar Kotun Jiha da huɗu daga Kotun ɗaukaka ƙara, sun sauya ranar haihuwarsu a cikin bayanan ɗaukar aiki a yunƙuri na tsawaita wa’adinsu a kan benci shari’a ba bisa ƙa’ida ba.

Alƙalan da abin ya shafa daga babbar kotun jihar Imo su ne Mai Shari’a M.E. Nwagboso, B.C. Iheka, K.A. Leaweanya, Chinyere Ngozi Okereke, da Innocent Chidi Ibeawuchi.

Daga kotun ɗaukaka ƙara, alƙalan da aka kora sun haɗa da Justice Tennyson Nze, Uchenna Ofoha, Eɓeryman Eleanya, da Rosemond Ibe.

A wani mataki na ladabtarwa, majalisar ta kuma tilasta mai shari’a T.N. Nzeukwu yin ritaya bisa amincewa da naɗin muƙaddashin babban alƙalin jihar Imo duk da kasancewarsa na huɗu a matsayi – matakin da ya saɓa wa sashe na 271 (4) na Kundin Tsarin Mulki na shekarar 1999.

Majalisar NJC ta sake jaddada umarnin da ta bayar tun farko ga Gwamnan Jihar Imo, Sanata Hope Uzodinma, na naɗa babban alƙali a shari’ar jihar a matsayin muƙaddashin babban alƙali, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

A halin yanzu, Mai Shari’a ɓ.U. Okorie, shugaban kotun ɗaukaka ƙara ta Imo, wanda ya jagoranci hukumar da ta bada shawarar mai shari’a Nzeukwu, an wanke shi daga aikata ba daidai ba, bayan da ya nuna rashin amincewarsa a lokacin naɗin.

A wani labarin kuma, majalisar NJC ta ba da shawarar a naɗa jami’an shari’a 21 a sassa daban-daban.

Daga cikinsu akwai: 

Mai Shari’a Adekanye Lekan Ogunmoye a matsayin babban alƙalin jihar Ekiti.

Kadi Abba Mammadi a matsayin Grand Kadi na Jihar Yobe.

Mainasara Ibrahim Kogo Umar, Esƙ. a matsayin shugaban kotun ɗa’ar ma’aikata.

Sauran shawarwarin sun haɗa da:

Babban Kotun Kuros Ribas: Edu Glory Bassey, Irem Melody Bassey.

Babban Kotun Ogun: Ojikutu Adebayo Julius, Adewole Adejumoke Oluwatoyin, Adebo Oluyemisi Olukemi.

Babban Kotun Zamfara: Garba Sirajo Aliyu, Bashir Rabi, Abdullahi Nasiru.

Kotun ɗaukaka ƙara ta Shari’a ta Zamfara: Ibrahim Jibril, Muhammed Sanusi Magami, Shaa’ban Mansur.

Kotun zaukaka ƙarar shari’ar Filato: Badamasi Kabir Adam.

Kotun zaukaka ƙara ta Ebonyi: Ogodo Lynda Nneka.

Babbar Kotun Katsina: Dikko Fadila Muhammad, Abdulrahman Shamsudden Yammama, Abdullahi Maryham Umaru, Mohammed Abubakar Dikko.

By ukarofi