Arteta na takarar zama gwarzon koci a Firimiya na watan Agusta

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Mikel Arteta na takarar gwarzon koci a Firimiya na watan Agusta, bayan da ya ja ragamar Arsenal wasa huɗu ba tare da an doke ƙungiyar ba.

Kocin ya doke Nottingham Forest da Crystal Palace da yin 2-2 da Fulham a dai gasar ta firimiya da haɗa maki bakwai a watan na Agusta.

Wannan ƙwazon na koci ya sa shi cikin koci biyar da ke takara kocin da ba kamarsa a watan na jiya.

Mikel, wanda ya lashe kyauta huɗu ta gwarzon koci a firimiya a bara na takara tare da Pep Guardiola na Manchester City, bayan da ƙungiyar ta ci dukkan wasa uku a watan Agusta.

Sauran ‘yan takara sun haɗa da Jurgen Klopp na Liverpool da David Moyed na West Ham da Ange Postecoglou na Tottenham, wanda ya ci wasa biyu da canjaras daya a watan jiya.

Ranar Lahadi Arsenal ta ci Manchester United 3-1 a wasan mako na huɗu a babbar gasar tamaula ta Ingila da suka fafata a Emirates.

Gunners tana mataki na biyar da maki 10 iri ɗaya da wanda Tottenham da Liverpool da West Ham keda shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *