Nasarorin da matar Gwamnan Kebbi ta samu cikin kwana 100 a ofis 

Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi 

Hajiya Zainab Nasir Idris (Nasare) matar Gwamnan Jihar Kebbi, wacce ake wa kirari da mace mai kamar maza da ke da burin canza rayuwar mabuƙata zuwa mawadata ta hanyar bayar da tallafi a inda ya dace.

Kasancewar ta matar gwamna, hakan bai hana ta ayyukan da ta taso tana aiwatarwa ba kafin yanzu.  

A cikin kwanaki 100 da ta yi na matar gwaman, Hajiya Nasare ta sami nasarar canza rayuwar mutane da yawa, musamman mabuƙata a faɗin jihar ta Kebbi, inda ta ba wa waɗansu damar kaiwa ga wani bagire da a baya ba sa tunanin kaiwa.

’Yan kwanaki kaɗan da shirgarta ofis ta nemi haɗin kan ƙungiyoyin mata da hukumomin da ke da alhakin kulawa da rayuwar mata da ƙananan yara da kuma marasa galihu da suka haɗa da Ƙungiyar Mata ’Yan Jarida (NAWOJ) da HILWA da da dai sauransu tare da haɗin kan ma’aikatar mata ta jihar. 

Tare da samun haɗin kan waɗannan ƙungiyoyin Hajiya Nasare ta sami nasarorin zama uwar ƙungiyoyi da kuma samun lambobin yabo da karramawa da yawa. 

Ƙirƙiro Nasara Foundation da ta yi kawo yau dubban mata da yara marasa galihu ne suka amfana da shi ta hanyar biyan kuɗin makarantun yara marayu, samar da ƙananan sana’o’i ga mata 300 da bayar da jari ga mata musamman zawarawa da ke riƙe da marayu.

Haka zalika a ƙarƙashin Nasara Foundation ana kai tallafi a sansanin ’yan gudun hijira da ke ƙaramar hukumar mulki ta Dankon/Wasagu lokaci-lokaci da kuma raba abinci da tufafi ga marayu da ke ƙananan hukumomin Gwandu da Suru da kuma Maiyama.

A ɓangaren lafiya wannan gidauniyar a wani hadingwiwa da NYSC an yi wa mutane 1200 aikin gyaran ido kyauta, mutane 1,247 aka yaye daga cibiyoyin koyon sana’o’i na Hajiya Nasare.

Yanzu haka za a faɗaɗa ayyukan wannan ƙungiyar ta hanyar ƙirƙiro waɗansu hanyoyi da a ke sa ran idan an bi su za cima nasarorin rage raɗaɗin matsin tattalin arziki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *