Asari ya sari ’yan Biyafara

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Duk lokacin da ka ke ƙoƙarin bambanta Ɗanjuma da Ɗanjummai sai ka duba dalilan da su ka saka aka kawo batun. Idan ana neman a nuna duk mutanen biyu ɗabi’ar su iri ɗaya ce ta kan iya yiwuwa ko zama mai ma’ana. A wasu ɓangarorin su na da bambanci. Mutumin da ya yi mari ya tsaya a nan da wanda ya yi mari ya tsinka jaka su na da bambanci amma sun haɗa hanya ta wannan marin da a ka yi. Idan marin bisa zalunci ne, sai a ce mutanen biyu sun zo ɗaya a aikata zalunci. Manufa ta a nan tsakanin tsohon ɗan tsageran Neja Dalta masu fasa bututun man fetur da Nnamdi Kanu mai ingiza kashe mutane da sunan kafa ƙasar Biyafara.

Dukkan mutanen biyu sun haɗa hanya wajen yi wa ƙasa zagon ƙasa. Tsagera na yi wa ƙasa zagon ƙasa ta hanyar karya tattalin arziki su kuma ’yan awaren Biyafara kan raba ƙasa mai ’yanci da aikata kisan gilla.

Mujahid Asari Dokubo tsohon kwamandan ’yan tsageran Neja Delta ne kuma ya kan yi bayanai wani lokacin masu amfani wani lokacin akasin haka. Gaskiya za a iya zaiyana kalaman Dokubo da tamkar hanjin jimina da na ci da na zubarwa. Asalin tsarin ’yan awaren Biyafara tun daga kan madugun su marigayi Odumegwu Ojukwu na ayyana yankin ƙasar da su ke son kafawa da ya haɗa da sashen kudu amso gabashin Nijeriya da kudu maso kudancin Nijeriya. Ba za a yi mamaki ba in wasu ’yan kudu maso gabashi sun mara baya ga Ojukwu don ɓangaren ta ta ta’allaka ne kan ƙabilanci.

A gefe guda kudu maso kudu ba za su iya biyewa Ibo ba indai a na maganar rinjayen ƙabila ne don su na da na su ƙabilun. Kazalika fargaba ta shiga zuciyar ’yan yankin cewa in aka kafa ƙasar Biyafara, Ibo masu rinjaye a kudu maso gabar za su mamaye madafun iko kuma ba za su yi mu su adalci ba. Wannan kancal ɗin na bambancin muradun ƙabila ya kawo cikas ga ƙarfin tunzurin neman kafa Biyafara.

A yanzu sabbin ’yan awaren Biyafara ƙarƙashin Nnamdi Kanu sun zaɓi hanyar kisan gilla ga musamman ’yan Arewa da ke zaune a yankin Kudu maso gabar ko kuma su ka je don ziyarar wani aiki. Hakanan su kan kona ofisoshin ’yan sanda da ma kashe jami’an tsaro. Alamu na nuna ’yan sabuwar tafiyar Biyafara wato IPOB na son amfani da zubar da jinin sauran ’yan ƙasa ne don a ce an gaji hakanan a bar su, su kafa ƙasar su.

Shin da gaske ne akasarin Igbo na son a kafa ƙasar Biyafara? Idan a ka ɗauki abin bisa tasirin ƙabilanci za a iya amincewa da haka ne akasarin su na mara baya ko da a cikin zuciya ne. Ibo ƙabilace da ta watsu a sassan Nijeriya jama’ar ta na gudanar da harkokin kasuwanci amma sai a ka samu wasu na neman lalata wannan zummar kasuwancin zuwa fitinar zubar da jini da bunƙasa wutar ƙiyayya tsakanin ’yan ƙasar da ke da bambancin addini, ƙabila da al’ada. Mafi munin fitina ita ce wacce kan shafi kashe rayukan mutanen da ba su yi wani laifi bisa ƙa’idar shari’a ba.

Wataƙila laifin su shi ne zama ’yan ƙabilar nan ko ’yan addinin can ko ’yan yankin can. Duk ƙasar da ta yi soko-soko a ka shigar da ƙiyayyar waɗannan lamuran uku, to sai yanda hali ya yi na makomar ta. Irin wannan kan haifar da yaƙin basasa da kasahe-kashen da ba gaira ba dalili. Abun ya zama wanda ya kashe ba shi da hujjar kisan ko ma ba shi da wata ribar kisan. Wanda a ka kashen bai san wane laifi ya yi da ya cancanci a kashe shi ba.

Don haka ƙasashe masu bambance-bambance, sai sun dage wajen samun shugabannin da ke da adalci ga kowa ba la’akari da son zuciya. Hakanan shugabannin su zama masu juriya da haquri da kuma ɗaukar matakin da ya dace a lokacin da ya dace kan duk wanda ya dace ko wanene kuma ko dan gidan waye ne. Wuta tun ta na ƙarama a kan kashe ta amma in a ka yi sakaci ta girma sai an gayyato motocin kashe gobara.

A kan iya samun cikas a kira motocin ya zama ba su da wadatar ruwa a lokacin da za a iya taɓukawa wajen kashe wutar. Irin misalin hoton abun da ke faruwa a Nijeriya kenan inda ta kan kai har ma mutane su riƙa ɗaukar doka a hannu. In a ka samu yanayin da mutane su ka samu sararin ɗaukar doka a hannu zai zama a na kisa ba tare da bincike ba. Kuma maimakon a kashe kawai sai ya kai ga yanke kai ko ƙona gawar wanda a ka kashen. Ma’ana fitar da rai ba ya wadatar da masu ɗaukar doka a hannu sai sun yi gangamin ƙona gawar wanda suka kashe sannan zuciyar su za ta iya gamsuwa cewa sun dau mataki. Idan an samu masu ɗaukar dokar kan manufa ce ta adalci, to da dama-dama. Me za a cewa masu ɗaukar doka a hannu ta hanyar son cimma burin son zuciya kamar neman raba ƙasa, ƙiyayyar addini ko ƙabilanci?

Tsohon kwamandan tsageran Neja Dalta Mujahid Asari Dokubo ya ce, munin ’yan awaren Biyarafa na IPOB ya fi na ƙungiyar ta’addanci. Dama gwamnatin Nijeriya ta aiyana ’yan awaren a matsayin ’yan ta’adda kamar Boko Haram da ɓarayin daji. Babu zayyanawa a yanzu ta mugun laifi da ya wuce ta’addanci.

Dokubo ya wallafa faifan bidiyo na kai tsaye a shafin sa na Fesbuk ya na caccakar ’yan IPOB da cewa shaiɗanu ne waɗanda munin aikin su ya fi na ƙungiyar ta’adda. Mujahid Dokubo ya ce matakin ’yan awaren na hana fita a yankin Kudu maso gabashin Nijeriya na hallaka tattalin arzikin yankin.

Caccakar ta Dokubo ta zo ma daidai lokacin da a ke zargin IPOB da kashe mutane da cin naman su, kamar yanda a ka gani a faifan wani bidiyo da ke nuna haramtattun miyagun sun  kashe wasu mutane su ka yanke kan su da hura wuta kamar masu gasa nama; su na yin wasu al’adu tamkar matsafa.

Wani ma ya kama hancin daya da kawunan biyu ya ce hancin Bafulatani ne don ya na da dogon hanci sabanin gajeren hanci mai faɗi.

Haƙiƙa ba tattalin arziki kadai ’yan awaren ke ruguzawa na yankin ba, har ma da ilimi don an ga wani faifan bidiyo na wasu yara sun fito don tafiya makarnta a ra nar da ’yan awaren su ka haramta fitowa.

Hakanan ’yan ta’addan su ka yi mu su barazana da harba bindiga su ka tilasta su kwave kayansu suka zama tsirara! Laifin yaran su na son yin karatu don samun ilimin da zai taimake su a rayuwar duniya. Har a ka kammala daukar faifan ba alamun an ceci yaran. Ba mu ma san me miyagun irin su ka yi wa yaran ba.

Kuma a ce duk wannan abun a Nijeriya ya ke gudana. Duk da tsagerancin ɗabi’a ta Dokubo amma wannan karo ya fito ya lura da yadda ’yan awaren ke yi wa kan su da kan su illa. Mugun mutum ba ya zama mafi mugunta sai ya yi wa kan sa. Ai mu na da labarin yanda ’yan ta’addan da su ka gawurta kan yi kisa a cikin gida kan iyaye da ’yan uwa, sai su koma kan abokai ba tare da yin nadama ba. Duk wanda zai kashe wanda bai yi ma sa laifin komai ba ya hau gado ya yi barci da minshari to wannan ya rasa digon Imani da tausayin ɗan-adamtaka.

Jaridar Daily Sun a makon jiya ta wallafa zantawa da babban dattijon yankin Ibo, Mbazulike Amaechi wanda ke cewa har yanzu bai sare ba, kan neman gwamnati ta sako Nnamdi Kanu da ke hannun jami’an tsaron DSS.

In za a tuna Amaechi ya jagoranci tawagar ’yan ƙabilar Ibo zuwa fadar Aso Rock inda ya buƙaci shugaba Buhari ya sako Kanu in ya so, su kuma dattawan Igbo za su dau matakin gyara ɗabi’un madugun raba kan ƙasar. Mbazulike Amaechi ya ƙara nuna cewa za a iya shawo kan taƙaddamar ta hanyar siyasa.

Kazalika tsohon mutumin wanda ya ke ganin Ibo na ɗaukarsa da darajar gaske, ya yi fatar ya ƙara nisan kwana tun da yanzu ya na wajajen 92 don ya samu ya daidaita yankin Ibo don kar ya mutu ya bar baya da ƙura. Tuni masu tambaya na yi cewa in har Aamechi na da tasiri me ya sa bai hana cigaba da kisan gilla da cin zarafin mutane da yara ’yan makaranta da IPOB ke yi ba. Aƙalla dai ya kamata waɗanda ke zaune a yankin su samu salamar gudanar da ayyukan su na yau da kullm in ya so batun neman raba ƙasa ya ci gaba da gudana a siyasance.

Ɗabi’ar waɗannan mutane fa ke sa sauran ’yan ƙasa fargabar a bar su, su mallaki ƙasar ta Biyafara don abun da zai biyo baya. Matuƙar kasa za ta yi makwabtaka da irin ƙasar da ‘yan IPOB ke mulka ai ba za a taɓa samun zaman lafiya ba. Hakan na nuna faɗan kan iyaka, cilla makamai masu linzami, jirgi marar matuƙi da baƙaƙen magana ta kafafen labarun farfaganda.