Daga AISHA ASAS
Annabin Rahma (S.A.W) ya ce, “Idan ku ka samu wanda ku ka yarda da halinshi, to ku ba shi aure………”
Ta yaya iyaye za ku iya gane halin mutum idan ba ku yi bincike ba?
Masu karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin Iyali na jaridar Blueprint Manhaja. Sannunku da jimirin bibiyarmu. Fatan Allah ya sa mu amfana da juna.
Bincike wani muhimmin abu ne ko ince ɗaya ne daga cikin tubali da ake gina aure kansa, kuma za mu iya amincewa da cewa, dukka malamai sun yi ijtima’i akan yin sa shi ne mafi a’ala akan auren da ake son yi don samun mazauni na dindindin.
Idan za mu yi duba ta ɓangaren iyaye na mace, musamman budurwa wadda ba ta yi hankalin sanin yadda za ta tunkare sha’anin aure da kuma sanin me yake ciki ba, wani haƙƙi ne kan iyaye na su yi ƙwaƙwaran bincike kan wanda za su miƙa wa ɗiyarsu aure, musamman ma kasancewarsa rayuwa da ake fatan ta zama mai ɗorewa.
Tambayata ta farko ga iyayen da ba sa bincike kafin su bada ‘ya’yansu, shin a ina suka samu wannan a addinin Musulunci? Koyarwa suke bi? Idan har sun ce kan hanya suke mene ne hujjar da suka yi riƙo da ita?
Duk uban da zai ba wa wani ‘yarsa wanda shi bai san halinsa ba kuma bai bincika ba, to tabbas ba watta hujja da zai iya kawowa a matsayin ƙwaƙwara da za ta iya kare shi a gaban mahaliccinsa.
Aure bai zama wani abu da ke buƙatar a sanya son rai a cikinsa ba, kuma ɗaya daga cikin dalilan da ke yawaita mutuwar aure akwai kawar da kai daga tsarin da Allah ya shirya. Babu inda Allah ya ce ka bayar da ‘yarka ga wanda ba ka da tabbacin zai iya riƙe ta, ko ga wanda ka ke da masaniyar zai iya cutar da ita.
Abin takaici ne yadda wasu iyaye ke sanya son rai da buƙatarsu a gaba yayin da za su bada auren ‘ya’yansu mata, ta yadda za su kawar da kai daga ganin aibu ko illa idan an zo masu da ita ta waɗanda suka yi nufin ba wa ‘ya’yansu mata. Kuma wannan ba koyarwar addini ba ce.
Idan kai uba ko uwa kuna tunanin ku kuka haifi ‘ya’yanku za ku iya yin yadda ku ke so da su, ina ku ka baro haƙƙin Allah na ba ku amanarsu da ya yi. Lallai Allah mai tambayarku ne akan yadda ku ka gudnanar da rayuwarsu.
A mizani na hankali, idan aka ce ‘yarka ta isa aure ko ta samu wanda take so ko yake sonta, kai uba kai ne za ka shiga ka fita don nemo halin wanda za ka haɗa zuri’a da shi wanda ake so ka yi iya yinka sai ka bar wa Allah saura.
Idan kunnenka ya jiyo mumuna daga cikin ababen da aka hane ku da ku ƙulla aure kansu, to ku yi gagawar kawar da zancen ku nema masu wani na ƙwarai daga wurn Allah, wannan shi ne mafi alkhairi a gare ku.
Idan ku ka sa son rai, kuma kuka rufe ido daga ganin gaskiya, to lallai za ku tsayu a gaban ubangijinku kuma zai yi hisabi a tsakaninku.
Shin abin tambaya gare ku ya ku iyaye, shin mene ne fatanku ga aurar da ‘ya’yanku? Zaman lafiya da kwanciyar hankali ko? To me ya sa kuke kawar da wannan don kawai son zuciya. Me ya sa ku ke saka naku ra’ayi a sama da na farin cikin ‘ya’yanku. Ku kwatanta da kanku, ku yi adalci gare su, shin idan ku ne a matsayinsu za ku iya auren mashayi? ko mazinaci? ko madargaci? ko makamacinsu daga munanan ɗabi’u? Idan kuwa ba za ku iya ba me ya sa su za ku so su da su? Me ya sa son zuciya zai rufe maku ido har ku kauce wa gaskiya da duk wanda ya ji zai sanyaku a jerin mutanen banza. Duk saboda son rai irin naku.
Wallahi ‘ya’yanku ba bayinku ba ne, amanar Allah ce, kuma shi masani ne akan abinda yake zukatanku da dalilin aikata abinda ku ka yi, ba abinda fatar bakinku ke faɗa ba, don haka zai iya kama ku akan zaluntan da ku ka yi wa ‘ya’yanku don biyan taku buƙata.
Za mu ci gaba.
