Muhimman amfanin man jojoba ga fata

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

Mai karatu sannunku da sake kasancewa da shafin Kwalliya na jaridar Blueprint Manhaja. A makon da ya gabata, mun yi shimfiɗa kan ɗaya dagacikin ababen tsiro masu matuƙar muhimmanci ga lafiyar fata, amma kuma ɓoyayyen abu musamman a ƙasar Hausa, wato man jojoba. 

A wannan mako za mu yi duba kan tasirin sa ga fata da kuma yadda za a ribatu da shi.

1. Shayar da fata ruwa tare da daidaita kitse:

Jojoba oil na samar da zurfin danshi ba tare da barin fata ta zama mai maiƙo ba. Saboda yana kwaikwayon sebum, wato yana aika saƙo ga fata ta rage yawan kitse da take fitarwa, wanda hakan ke taimaka wa wajen rage yawan mai a fuska. Ma’ana dai masƙin fuska zai ragu yayin amfani da shi, kuma hakan ba yana nufin fata za ta bushe ba.

2. Ba ya toshe ramukan fata (Non-Comedogenic):

Wannan sinadari yana daga cikin waɗanda ba sa toshe pores, wanda ke nufin yana da aminci sosai ga masu fama da kuraje ko fata mai saurin kumburi. Abin nufi babban makami ne na yaƙar ƙuraje da kuma matsalar kumburin fata.

3. Yaƙi da tsufa da lalacewar fata:

Yana ɗauke da sinadarin Vitamin E mai ƙarfi, wanda ke yaƙi da abinda ake kira da ‘oxidative stress’, wato lalacewar da rana, iska mai gurbatawa da sauran abubuwa ke haifarwa. A ɓangaren tsufa kuwa yana taimaka wa wajen rage bayyanar layukan tsufa (fine lines) da kuma yaƙunewa da fata ke yi albarkacin shekaru masu yawa.

4. Yana kwantar da fata tare da warkar da ita:

Kasancewar man jojoba yana da sinadaran rage kumburi (anti-inflammatory), yana taimaka wa wajen sassauta matsaloli irin su ƙesfi (eczema), rosacea, da kuma fata mai ƙaiƙayi, bushewa ko jin zafi.

By ukarofi