Babaji

5689 Posts

Kwankwaso ya bar NNPP a hukumance

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rahotanni sun bayyana cewa tsohon gwamnan Jihar Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Rabi'u Musa Kwankwaso ya bar jam’iyyar NNPP hukumance. Hakan na zuwa ne ƙasa da kwana ɗaya da ake sa ran zai koka ADC, wato a gobe Litinin. Kwankwaso ya ɗauki wannan mataki ne yayin da ake ta muhawara kan sauya sheƙar da wasu ‘yan siyasa ke yi saboda rikice-rikicen cikin jam’iyya. A sanarwar da ya fitar a yau Lahadi Kwankwaso ya bayyana godiyarsa ga jam'iyyar da jagorancinta bisa damar da ta ba shi na kasance jigo kuma jagora acikinta. A shekarar 2023 ne…
Read More

Kano: Gwamna Abba ya yi gargaɗin karkatar da tallafin tamowa da jakunkunan ɗalibai

Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta Jihar Kano, ta koka a kan sama da faɗi da ake yi da madarar tamowa ta ƙananan yara masu larurar rashin abinci mai gina jiki tare da handame jakunkunan ɗalibai da ke yankunan ƙananan hukumomi 44 na faɗin jihar. A bisa haka gwamnatin, ta gindaya doka da oda mai ƙarfi ga dukkan waɗanda suke da alhaki wajen karkatar da irin waɗannan muhimman kayayyakin tagomashin inganta rayuwar al'umar dake kafatanin jihar. Jami'in Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa Reshen jihar Kano, Malam Balarabe Yusuf Sani, ya nuna damuwa bisa yadda rashin gaskiya da amana suka mamaye…
Read More

Samson Adamu ya zama ɗan Nijeriya na farko da aka taɓa ba sakatare a Hukumar CAF

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ɗan Nijeriya Samson Adamu kuma shugaban hukumar gudanarwar ƙwallon ƙafar Nijeriya ya zama sabon Babban Sakataren Hukumar Kula da Ƙwallon ta Afirka, CAF. Wannan na zuwa ne bayan tsohon sakatare, Veron Mosengo-Omba daga Jamhuriyar Dimukraɗiyyar Kongo Democratic ya yi murabus daga muƙamin. Wannan na nuna ƙaruwar tasirin Nijeriya a harkar ƙwallon ƙafa ta Nahiyar Afirka. Gabanin naɗin nasa, Adamu shi ne Daraktan gasa da taruka na CAF. Kwamitin zartarwar CAF ne ya bayar da sunan ɗan Nijeriyar busa la'akari da gogewarsa a fannin ƙwallon ƙafa a wani zama da ya gudanar a Kairo, babban…
Read More

Tauraron Brazil da Real Madrid, Vinicius ya samu rauni

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tawagar ƙwallon ƙafar Brazil da Real Madrid na fuskantar matsalar babban giɓi sakamakon rauni da ɗan wasa Vinicius Junior ya samu. Wannan a'amari na zuwa ne yayin da 'yan wasan Brazil suke atisayen shirin gabanin wasan kawance da ƙasar za ta yi da Croatia. Hakan na zuwa ne tun bayan wasan da Faransa ta casa Brazil da ci 2 da 1 a makon da ya gabata inda Vinicius soma fama da ciwon damtse. An ga yadda 'yan wasan Brazil suka fito atisaye a Orlando a jiya Asabar ba tare da ɗan wasan ba. Hakan…
Read More

Kwankwaso da magoya bayansa na shirin koma wa ADC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Litinin, 30 ga watan Maris, 2026 ne ake sa ran jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso zai koma jam'iyyar adawa ta ADC. Rahotanni daga sahihan majiyoyi sun bayyana cewa tsohon gwamnan na jihar Kano na shirin ficewa daga jam’iyyarsa ta NNPP tare da koma wa ADC. Majiyoyin sun shaida wa DAILY NIGERIAN cewa wannan mataki na zuwa ne bayan shafe makonni ana tattaunawa tsakanin Kwankwaso, ƙungiyarsa ta Kwankwasiyya, da shugabannin jam’iyyar ADC domin cimma matsaya. Ana kallon wannan sauyi a matsayin babban ci gaba a siyasar Nijeriya, musamman duba da tasirin…
Read More

Muhimman abubuwan da Tinubu ya faɗa a taron APC na ƙasa

Yayin da ake cigaba da tunkarar babban zaɓen 2027, Jam'iyyar APC ta gudanar da babban taronta na ƙasa jiya a Abuja inda ta zaɓi sabbin shugabannin jam'iyyar, ga cikakken jawabin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wajen taron. "A yau, ina tsaye a gabanku zuciyata cike da godiya, alfahari, da fata. Godiya ga Allah Maɗaukaki saboda ni’imarsa ga ƙasarmu da jam’iyyarmu. Alfahari da abin da muka gina tun 2013, da kuma fatan makoma mai kyau duk da ƙalubalen da muke fuskanta. Wannan taron na APC karo na huɗu ba kawai taro ba ne; wani muhimmin babi ne a tarihin…
Read More

2026: WAEC ta fitar da sakamakon jarrabawar WASSCE na kwamfuta

A sanarwar da mukaddashin shugaban hulɗa da jama’a na hukumar, Moyosola F. Adesina ya fitar daga hedikwatar WAEC da ke Yaba, ya ce an gudanar da jarabawar ne a cibiyoyi 166 a faɗin Najeriya daga 28 ga Janairu zuwa 14 ga Fabrairu 2026. Jimillar ɗalibai 10,480 ne suka rubuta jarabawar, daga ciki dalibai 3,429 kashi 32.72% sun samu credit a akalla darussa biyar ciki har da Turanci da Lissafi. Wannan ya nuna ƙaruwa da kashi 5.76% idan aka kwatanta da sakamakon shekarar 2025 wanda ya kai 26.96%. Haka kuma, dalibai 43 masu buƙata ta musamman sun shiga jarabawar, inda WAEC…
Read More

Gidauniyar Kannywood ta yi jimamin rasuwar Aliyu Sambo

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gidauniyar Kannywood Ta yi alhinin rasuwar Aliyu Sambo, wanda ɗaya ne daga cikin dattawan masana’antar Kannywood kuma ɗaya daga cikin manyan jami’anta masu barin gado. Ta ce, marigayin yi taka rawa a wasannin kwaikwayo na dabe da kuma na talbijin sannan kuma ya taka rawa a wasannin kwaikwayo mai dogon zangon na Kwana Casa’in da kuma Zaɓi biyu a kwanan nan. A wata sanarwa da Daraktan yaɗa labaran gidauniyar, Yakubu Liman ya fitar, gidauniyar ta bayyana cewa marigayin ya kasance mai jajircewa da aiki tuƙuru da kuma nuna halayya na gari a mu’amalarsa da…
Read More

2027: Kwankwaso da Aregbesola sun gana a Abuja kan yiwuwar shiga ADC

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya gana da sakataren jam’iyyar ADC na ƙasa, Rauf Aregbesola, a birnin Abuja, lamarin da ke ƙara janyo hasashe a fagen siyasar Najeriya gabanin zaɓen shekarar 2027. Rahotanni na cewa ana rade-radin cewa jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa na duba yiwuwar komawa jam’iyyar ADC a wani ɓangare na sabuwar haɗakar siyasa da ake shirin yi kafin zaɓen gaba. Haka kuma, wasu rahotanni sun ce ana maganar yiwuwar haɗakar siyasa tsakanin Kwankwaso da tsohon gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, domin tsayawa takarar shugaban ƙasa tare a zaɓen 2027. Sai dai har yanzu babu wata…
Read More

An sake zaɓen Yiltwatda da Basiru a matsayin shugaba da sakataren jam’iyya a babban taron APC na ƙasa

An sake dawo da Farfesa Nentawe Yilwatda a matsayin Shugaban Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙasa, yayin da Surajudeen Basiru ya zama Sakataren jam’iyyar, bayan babban taron jam’iyyar da aka gudanar a daren Juma’a a Eagle Square da ke Abuja. Rahotanni sun nuna cewa Yilwatda, wanda tsohon Ministan Agajin Gaggawa ne, ya samu goyon bayan manyan jiga-jigan jam’iyyar daga sassa daban-daban na ƙasar nan kafin a tabbatar da shi a kan kujerar shugabanci. Kwamitin zartarwa na jam’iyyar (NEC) ya sanar da sakamakon ne a wani zama da aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa. An bayyana cewa Gwamnan Jihar Imo…
Read More