Babaji

5689 Posts

‘Yan bindiga sun halaka mutane uku da ƙone gidaje da rumbuna a Zamfara

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar 'yan sandan Jihar Zamfara ta ce wasu 'yan bindiga sun kai hari ƙauyen Ɗangoro da ke gundumar Nahuche a Ƙaramar Hukumar Bungudu, inda suka kashe mutane uku tare da lalata gidaje da wasu kadarori. Al'amarin ya auku ne da misalin ƙarfe 10:30 na daren ranar Asabar wayewar Lahadi. 'Yan bindigar sun shigo ƙauyen ne dauke da bindigogi ƙirar AK-47, inda suka riƙa harbe-harbe tare da cinna wa gidaje da rumbunan abinci wuta. Jami'an 'yan sanda da haɗin gwiwar dakarun sa-kai (Vigilante) sun isa wurin cikin sauri, inda aka gwabza faɗa da 'yan bindigar…
Read More

El-Rufa’i ya koma kotu bayan jana’izar mahaifiyarsa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya koma gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna domin sauraron buƙatar bayar da belinsa. Hukumar ICPC ce ta gurfanar da shi a gaban Mai shari’a Rilwan M. Aikawa akan tuhume-tuhume guda 10 da suka haɗa da zargin karkatar da kadarorin gwamnati da kuma zamba a lokacin da yake gwamnan jihar. Rahotanni sun bayyana cewa, an sako shi daga tsare ne a baya-bayan nan bisa rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Umma El-Rufai, wadda ta rasu a birnin Cairo na ƙasar Masar a ƙarshen makon da ya gabata. A baya dai…
Read More

Gawuna ya gana da Kwankwaso bayan barin APC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon mataimakin gwamna kuma ɗan takarar gwamnan Jihar Kano a zaɓen 2023, Nasiru Gawuna ya fice daga jam'iyyar APC a hukumance. Ana sa ran wannan matakin zai kawo sauyin alƙiblar siyasar Gawuna musamman bisa la'akari da sauye-sauyen jam'iyya acikin 'yan siyasa yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2027. Gawuna ya fice daga jam'iyyar APC ne bayan ya ajiye muƙaminsa na shugabancin bankin lamuni na ƙasa (FMBN). Duk da cewa Gawuna bau bayyana matakin siyasarsa ba na gaba, majiyoyi da dama na kusa da tsohon maitaimakin gwamnan sun bayyana cewa ya gana da tsohon gwamnan…
Read More

INEC ta amince da shugabancin PDP tsagin Wike

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta amince da Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) na jam’iyyar adawa ta PDP ƙarƙashin jagorancin Abdulrahman Mohammed, wanda tsagin Ministan Abuja Nyesom Wike ne. Bincike ya nuna cewa a shafin yanar gizon INEC, an ambaci Mohammed a matsayin shugaban PDP na kasa, tare da sauran mambobin kwamitin da suka hada da sakataren jam’iyya, Samuel Anyanwu, da sauran shugabanni. Wannan mataki na zuwa ne kwana guda bayan jam’iyyar PDP ta gudanar da babban taronta na kasa a Moshood Abiola National Stadium da ke birnin tarayya Abuja, inda wakilai sama da…
Read More

Yusuf Tuggar ya ajiye muƙamin ministan harkokin waje don tsaya wa takarar gwamna a Bauchi

Ministan Harkokin Waje, Yusuf Maitama Tuggar, ya yi murabus daga gwamnatin Bola Ahmed Tinubu domin tsayawa takarar gwamnan Jihar Bauchi a zaɓen 2027. Rahotanni sun nuna cewa ya miƙa takardar murabus ɗinsa ne a ranar Litinin bisa umarnin gwamnati na wajabta wa duk masu muƙaman siyasa da ke da burin tsayawa takara su sauka kafin ranar 31 ga Maris, 2026. Ana sa ran Tuggar zai tsaya takara ne a ƙarƙashin jam’iyyar All APC, matakin da ake ganin zai ƙara zafafa fafatawar neman kujerar gwamna a jihar Bauchi. Ficewarsa na daga cikin jerin murabus da ake sa ran za su biyo…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Kwankwaso ya koma ADC a hukumance

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana komawarsa jamʼiyyar adawa ta ADC a hukumance. Kwankwaso ya shelanta haka ne a yayin wani taro da aka gudanar gidansa da ke Kano. Tsohon gwamnan na Kano ya kuma buƙaci magoya bayansa da su yi rajistar jamʼiyyar, tare da samun katin zaɓe na ƙasa. Da fari, a juya Lahadi ne Kwankwaso ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar NNPP a hukumance a wata takarda daga gare shi. Ya bayyana cewa, ya ɗauki matakin ne bisa la'akari da sauyin akalar siyasar Nijeriya, wanda a cewarsa ya sa ya…
Read More

PDP tsagin Wike ta naɗa sababbin mambobin kwamitin jagorancin jam’iyyar

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Baki ɗaya 'yan takarar da suka nemi muƙamai daban-daban a matakin ƙasa na jam'iyyar PDP a yammacin ranar Asabar sun yi nasara bayan naɗin yarjejeniya da aka yi musu a babban taron jam'iyyar na ƙasa. Tsohon shugaban riƙo na kwamitin ayyuka na jam'iyyar (NCWC), Abdulrahman Mohammed ya zama na dindindin a muƙamin, inda kuma ake sa ran zai jagoranci tafiyar da harkokin NWCn na wasu shekaru huɗu nan gaba. Ga jaddawalin waɗanda aka naɗa a muƙaman kamar yadda Blueprint.ng ta ruwaito: "NATIONAL CHAIRMAN HON. ABDULRAHAMAN MOHAMMED DEPUTY NATIONAL CHAIRMAN (SOUTH) AARON CHUKWUEMEKA DEPUTY NATIONAL…
Read More

Sojoji sun halaka babban Kwamandan ISWAP, Al-Muhajir a Malam Fatori

Ƙungiyar ISWAP ta tabbatar da mutuwar wani babban mambanta na Majalisar Shawara (Shura Council), mai suna Abu Yahya Al-Muhajir, inda ta bayyana hakan a matsayin bbabban ashi ga ƙungiyar. An bayyana hakan ne a cikin wata takardar yaɗa farfaganda da ƙungiyar ta fitar, inda ta yi alhinin rasuwar sa tare da kiran mutuwar tasa a matsayin “mafi girman rashi a kwanakin A kwanan nan ne a yankin Malam Fatori majiyoyin tsaro sun ce ana danganta Al-Muhajir da hare-haren da aka kai a yankin Tafkin Chadi (Lake Chad Basin), Saidai har yanzu ba a tabbatar ko an kashe shi ne yayin…
Read More

Tinubu ya sadaukar da baki ɗaya albashinsa ga sojoji tun bayan zama shugaban ƙasa

Shugaba Bola Tinubu ya sanar da kafa wani asusun tallafi na musamman domin taimaka wa sojojin Nijeriya musamman waɗanda suka jikkata a bakin aiki da kuma iyalan waɗanda da suka rasa rayukansu bai wa ƙasa kariya. Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi yayin bikin cikar sa shekaru 74 da haihuwa, inda ya ce wannan mataki wata hanya ce ta girmama jarumtaka, sadaukarwa da hidimar da sojoji ke yi wa kasa. A cewar sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu ya umarci Akanta-Janar na Tarayya da ya bude wani asusu na musamman domin…
Read More

Uba Sani, Pantami, Ɗangote, Atiku da wasu sun halarci jana’izar mahaifiyar El-Rufa’i a Abuja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Birnin Tarayya Abuja ta cika da sanannun 'yan siyasa a jiya Lahadi yayin da aka yi jana'izar Hajiya Umma, mahaifiyar tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai. An sallace ta ne a babban masallacin Juma’a na ƙasa dake Abuja, inda aka haɗu wajen yi mata addu'o'in fatan samun rahamar Allah. Cikin waɗanda suka halarci sallar akwai Alhaji Aliko Ɗangote, Sarki Sanusi Lamido Sanusi II, NSA Nuhu Ribadu, Atiku Abubakar, Gwamna Senator Uba Sani , Gwamna Zulum, Bago, Abdulazeez Yari da sauran tsofaffi da shuwagabanni, Gwamnoni, Sanatoci, Sarakuna, Yan kasuwa da sauran su. Da fari…
Read More