INEC ta amince da shugabancin PDP tsagin Wike

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta amince da Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) na jam’iyyar adawa ta PDP ƙarƙashin jagorancin Abdulrahman Mohammed, wanda tsagin Ministan Abuja Nyesom Wike ne.

Bincike ya nuna cewa a shafin yanar gizon INEC, an ambaci Mohammed a matsayin shugaban PDP na kasa, tare da sauran mambobin kwamitin da suka hada da sakataren jam’iyya, Samuel Anyanwu, da sauran shugabanni.

Wannan mataki na zuwa ne kwana guda bayan jam’iyyar PDP ta gudanar da babban taronta na kasa a Moshood Abiola National Stadium da ke birnin tarayya Abuja, inda wakilai sama da 2,000 daga jihohi 36 suka halarta.

Ga jaddawalin ‘yan kwamitin kamar yadda NewsPointNigeria ta ruwaito:

“Abdulrahman Mohammed — National Chairman
Aaron Chukwuemeka — Deputy National Chairman (South)
Yusufu Akirikwen — Deputy National Chairman (North)
Anyanwu Samuel — National Secretary
Kolawale Olabisi — Deputy National Secretary
Odeyemi Oladiran — National Treasurer
Lado Marke — Deputy National Treasurer
Eyim Henry — National Financial Secretary
Grema Kyari — Deputy National Financial Secretary
Umar Bature — National Organising Secretary
Efere Augustine — Deputy National Organising Secretary
Jungudo Mohammed — National Publicity Secretary
Egwu Chidiebere — Deputy National Publicity Secretary
Kamaldeen Ajibade — National Legal Adviser
Aloysius Uba — Deputy National Legal Adviser
Osuoha Donatus — National Auditor
Adaba Seri Yatu — Deputy National Auditor
Ogunshe Adedayo — National Women Leader
Hauwa Shinge — Deputy National Women Leader
Ibrahim Aboki — National Youth Leader
Momoh Bashir — Deputy National Youth Leader.”

By Babaji