Yusuf Tuggar ya ajiye muƙamin ministan harkokin waje don tsaya wa takarar gwamna a Bauchi

Spread the love

Ministan Harkokin Waje, Yusuf Maitama Tuggar, ya yi murabus daga gwamnatin Bola Ahmed Tinubu domin tsayawa takarar gwamnan Jihar Bauchi a zaɓen 2027.

Rahotanni sun nuna cewa ya miƙa takardar murabus ɗinsa ne a ranar Litinin bisa umarnin gwamnati na wajabta wa duk masu muƙaman siyasa da ke da burin tsayawa takara su sauka kafin ranar 31 ga Maris, 2026.

Ana sa ran Tuggar zai tsaya takara ne a ƙarƙashin jam’iyyar All APC, matakin da ake ganin zai ƙara zafafa fafatawar neman kujerar gwamna a jihar Bauchi.

Ficewarsa na daga cikin jerin murabus da ake sa ran za su biyo baya, sakamakon umarnin da aka bayar ta ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, wanda ya shafi duk masu muƙaman siyasa da ke son tsayawa takara.

Majiyoyi sun ce ƙwarewar Tuggar a difulomasiyya da muƙamin minista na iya ba shi fa’ida a siyasar Bauchi, musamman wajen samun goyon baya da kuma faɗaɗa alaƙa.

Ana sa ran ƙarin murabus daga sauran jami’an gwamnati yayin da ƙarewar wa’adin da Shugaba Bola Tinubu ya bayar ke ƙaratowa.

By Babaji