
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana komawarsa jamʼiyyar adawa ta ADC a hukumance.
Kwankwaso ya shelanta haka ne a yayin wani taro da aka gudanar gidansa da ke Kano.
Tsohon gwamnan na Kano ya kuma buƙaci magoya bayansa da su yi rajistar jamʼiyyar, tare da samun katin zaɓe na ƙasa.
Da fari, a juya Lahadi ne Kwankwaso ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP a hukumance a wata takarda daga gare shi.
Ya bayyana cewa, ya ɗauki matakin ne bisa la’akari da sauyin akalar siyasar Nijeriya, wanda a cewarsa ya sa ya ga dacewar sabunta tafiyar siyasarsa.
Waɗanda suak halarci taron sun haɗa da Shugaban jam’iyyar kuma tsohon shugaban majalisar dattawa David Mark; Sanata Aminu Tambuwal, Rotimi Amaechi, Peter Obi, Sanata Dino Melaye, da kuma tsohon shugaban jam’iyyar APC, John Odigie-Oyegun da dai sauransu.

