‘Yan sanda sun tabbatar da kisan mutane 14 a harin ‘yan bindiga a Jos

Spread the love

Daga HABU ƊAN SARKI a Jos

Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Filato ƙarƙashin jagorancin Kwamishina Bassey Ewah ta tabbatar da mutuwar mutane 14 a sakamakon harin ‘yan bindiga a mashayar Gari Ya Waye da ke Anguwar Rukuba cikin ƙaramar hukumar Jos ta Arewa.

A wata sanarwa da ta fito daga ofishin Kwamishinan ‘yan sandan an bayyana cewa mutane 12 ne aka tabbatar da mutuwar su cikin daren jiya, a cikin su har da mata guda biyu. Sai zuwa safiyar yau kuma an ƙara gano gawarwarki biyu a wasu lunguna na unguwar, yayin da jami’an tsaro ke bin sawun maharan, wanda ya sa adadin waɗanda suka mutu suka kai 14.

Ko da yake bayanan da mutanen unguwar ke fitarwa na cewa, adadin mutanen da suke zargin an kashe sun haura 30.

Yayin da yake jajentawa al’ummar Anguwar Rukuba da wannan mummunan hari ya shafa, kwamishinan ya roƙi jama’a su yi haƙuri su kwantar da hankali, su guji ɗaukar doka a hannu. Ya kuma ƙara da cewa, haɗin gwiwar jami’an tsaro na ‘yan sanda da sauran rundunonin tsaro na gudanar da aikin samar da tsaro, da zaman lafiya.

Ya buƙaci jama’a a ƙaramar hukumar Jos ta Arewa su bai wa jami’an tsaro haɗin kai da taimaka musu da muhimman bayanai da za su basu damar gano maɓoyar duk wasu ɓatagari, domin hukunta su.

By ukarofi