Babaji

5689 Posts

Kashe-kashen Filato: Tinubu ya dakatar da tafiya Ogun, zai garzaya Jos yayin fara ziyarar jihohi huɗu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Laraba Shugaba Bola Tinubu ya sanar da dakatar da shirinsa na tafiya Iperu da ke Jihar Ogun, inda ya bayyana cewa a halin yanzu babban aikinsa shi ne tsayawa tare da al’ummar Jihar Filato sakamakon hare-haren da suka yi sanadiyyar asarar rayuka da dama. A sanarwar da ya fitar, Shugaban ƙasar ya ce zai ziyarci birnin Jos domin jajenta wa iyalan da suka rasa ‘yan uwansu, tare da sake jaddada cewa masu ƙoƙarin tayar da zaune-tsaye a ƙasar ba za su yi nasara ba. Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin tarayya za…
Read More

Kotu ta ayyana 14 ga Afrilu a matsayin ranar hukunci akan buƙatar belin El-Rufa’i

Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna, ta sanya ranar 14 ga watan Afrilu, 2026 domin yanke hukunci akan buƙatar beli da tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya gabatar. A yau Laraba ne lauyoyin El-Rufa’i da masu gabatar da ƙara wato hukumar ICPC suka gabatar da hujjojinsu a gaban kotun da ke Kaduna domin duba batun bukatar ba da tsohon gwamnan na jihar Kaduna beli. Babban lauyan masu kare El-Rufai, Adewole Iyamu, ya bayyana cewa suna da kwarin gwiwar samun sakamako mai kyau, yana mai cewa sun gabatar da dukkan hujjojinsu yadda ya kamata a gaban kotu. Ya tabbatar…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Mutane da dama sun rasu yayin da sabon rikici ya ɓarke a Jos

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An sake shiga fargaba a wasu sassan Jihar Filato yayin da wani sabon rikicin ya ɓarke, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama. Rikicin na zuwa ne sa'o'i kaɗan bayan da gwamnatin jihar ta ɗage dokar ta-ɓaci ta sa'o'i 48 da aka kafa tun da fari, biyo bayan wani hari da wasu mahara sanye da kayan soja suka kai wa al'ummar yankin Rukuba a ranar Lahadi. Rahotanni sun bayyana cewa 'yan unguwar Unguwar Rukuba da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa sun riƙa kai wa juna farmaki a yau Laraba. Shaidu sun ce,…
Read More

Ministan Lantarki, Adelabu ya musanta yin murabus daga muƙamin

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ministan Lantarki, Adebayo Adelabu ya musanta rahotannin da ke cewa ya ajiya muƙaminsa na minista, yana mai bayyana su a matsayin ƙarya da aka ƙirƙira da nufin ruɗar da jama'a yayin da ake raɗaɗi akan goben siyasarsa. Hakan na zuwa ne a daidai da Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarni ga masu riƙa da muƙamai acikinta da ke son tsayawa takara a zaɓen 2027 da su ajiye muƙamin da akabasu. Da yake tsokaci akan al'amarin a wata hirar WhatsApp da manema labarai a jiya Talata, mai taimaka wa Adelabu akan harkokin yaɗa labarai, Bolaji…
Read More

Tinubu ya gayyaci Gwamnan Filato da jagororin tsaro kan harin Jos

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya gayyaci Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, tare da manyan jagororin tsaro zuwa Abuja sakamakon sabon harin kisan gilla da ya auku Unguwar Rukuba da ke garin Jos. Za a yi zaman ne domin yin nazari akan halin tsaro da ɗaukar matakan da suak dace wajen kare sake aukuwar irin haka a nan gaba. Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya bayyana cewa taron na da nufin tsara ingantaccen mataki na haɗin gwiwa domin magance rikicin tare da dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a jihar. Ya kuma yi kira ga al'umma…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Ministan Lantarki, Adelabu ya yi murabus

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ministan Wutar Lantarkin Nijeriya, Adebayo Adelabu ya yi murabus daga muƙaminsa a hukumance domin mayar da hankali akan neman takarar gwamnan jiharsa ta Oyo. A yau Talata Adelabu ya miƙa takardar yin murabus ɗinsa zuwa ga Shugaba Bola Tinubu ta hannun sakataren gwamnati. Acikin wasiƙar, ya yi godiya ga Shugaba Tinubu bisa damar da ya ba shi ta yi wa ƙasa hidima, yana mai cewa ya ji daɗin gudunmawar da ya bayar wajen inganta ɓangaren wutar lantarkin Nijeriya. A cewarsa, a yanzu hankalinsa zai karkata ne i'zuwa tsaya wa takarar gwamna a Oyo yayin…
Read More

Yanzu-yanzu: El-Rufa’i ya koma hannun ICPC bayan bayyana a gaban kotu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A yau Talata ne aka sake mayar da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai hannun Hukumar Yaƙi da Rashawa (ICPC) domin ta cigaba da tsare shi bayan sakin sa na wasu kwanaki da aka yi a makon da ya gabata kan rasuwar mahaifiyarsa. Rahotanni sun bayyana yadda aka sake gurfanar da shi a gaban kotu a yau, inda ya fara bayyana a Babbar Kotun Tarayya ta Jihar Kaduna akan wani sabon zargi da ICPC ta shigar a kansa. Saidai rashin halartar wanda ake ƙara tare da shi ya sa aka ɗage sauraron ƙarar zuwa…
Read More

Yanzu-yanzu: Gawuna ya koma ADC a hukumance

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An samu sabon sauyi a tafiyar da harkokin siyasar Kano yayin da tsohon ɗan takarar gwamnan Jihar na jam'iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna ya koma jam'iyyar adawa ta ADC a cigaba da shirye-shiryen zaɓen 2027. Rahotanni sun bayyana cewa, Gawuna ya yi rajista tare da karɓar katinsa na zama mamba a Gundumarsa ta Gawuna da ke Ƙaramar Hukumar Nassarawa a wani yanayi da dubunnan magoya baya da masu ruwa da tsaki suka shaida. Nasiru Gawuna shi ne tsohon mataimakin gwamnan jihar har na tsawon shekaru huɗu da watanni takwas, wato daga Satumbar 2018 zuwa…
Read More

Sheikh Abduljabbar ya yi wa Kotun Ƙoli ƙorafin tauye ‘yancinsa na ɗaukaka ƙara

Fitaccen malamin addini a Kano, Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara, ya miƙa ƙorafi ga Alƙalin Alƙali na Ƙasa (CJN), Kudirat Kekere-Ekun, inda ya yi zargin cewa ana jinkirta shari’ar ɗaukaka ƙarar da ya shigar ga gangan tare da wasu kura-kurai a tsarin gudanar da shari’ar. Ƙorafin, wanda aka shigar ƙarƙashin lambobin shari’a CA/KN/01/2025 da K/93CA/2022, ya buƙaci Alƙalin Alƙalai na Ƙasa da ya tabbatar da cewa an gudanar da shari’ar cikin adalci da kuma gaggawa. A cikin wasiƙarsa, Sheikh Kabara ya nuna damuwa kan wasu tangarɗa na gudanarwa da yake zargin suna kawo tsaiko ga shari’ar, da kuma wahalar samun cikakkun…
Read More

Iran ta harba makamai a Gabas ta Tsakiya yayin da Trump ya yi barazanar babbake masarrafar manta

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Iran ta kai sababbin hare-hare a yankin Gabas ta Tsakiya a yau Talata yayin da babban birninta ya fuskanci farmaki bayan Shugaba Donald Trump ya yi barazanar babbake masarrafar manta. Fraministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, wanda abokin Trump ne a kai wa Iran hare-hare, ya ce ya cimma sama da rabi na buƙatun sojin ƙasarsa duk da cewa kawo yanzu shugabannin biyu ba su cimma matsayar lokacin da za a kawo ƙarshen yaƙin wanda aka shafe sama da wata guda ana fafatawa ba. A wani labarin kuma, Donald Trump ya bayyana cewa ƙasarsa na iya…
Read More